‘Dan Najeriya mai shekara 8 yayi fice wajen wasan Chess a Amurka

‘Dan Najeriya mai shekara 8 yayi fice wajen wasan Chess a Amurka

Tanitoluwa Adewumi, wani yaro ne ‘Dan Najeriya mai shekaru 8 a Duniya, da Iyayen sa su ka tattara su ka koma kasar Amurka da zama kwanakin baya bayan ‘yan ta’addan Boko Haram sun fitine su.

Yanzu wannan yaro Tanitoluwa Adewumi yana cigaba da shahara a Amurka saboda irin kwarewar da yayi a bangaren wasan katin nan da ake yi da ake kira Chess da Ingilishi. A cikin shekara guda wannan yaro ya kware a wasan na Chess.

Nicholas Kristof na Jaridar New York Times ta kasar Amurka ya kawo labarin yadda Tanitoluwa Adewumi yake nema ya gagari duk wani mai buga wasan Chess. A cikin ‘yan kwanakin nan an rasa samun wanda zai iya doke Adewumi.

Adewumi mai shekara 8 ya lallasa duk sa’annin sa a makaranta da kuma mutanen Yankin Birnin New York a wannan wasa na kati. Ta dai kai cewa yanzu wannan karamin yaro ya lashe kofuna 7 na gasar Chess da ya buga a kasar Amurka.

KU KARANTA: Amurka ta bankado wasu manyan zunuban Gwamnatin Najeriya

‘Dan Najeriya mai shekara 8 yayi fice wajen wasan Chess a Amurka
Tanitoluwa Adewumi ya zama Tauraro a kaf Birnin New York
Asali: Depositphotos

Sai dai kuma duk da wannan, Nicholas Kristof yace wannan yaro yana cikin halin Ni-‘ya su ne a Amurka inda shi da Iyayen su ke barar mazukuni a cikin Unguwar nan na Manhattan da ke Birnin New York, bayan sun gudo daga Najeriya kwanaki.

A cikin lokaci kankani dai wannan yaro ya koyi wasan, ya kuma gawurta a Amurka duk karancin shekarun sa. Adewumi yana da maki 1587 na kwarewa, inda wanda ya fi kowa iya wasan a Duniya watau Magnus Carlsen yake kan maki 2845.

Sunan Mahaifiyar wannan yaro Oluwatoyin Adewumi, wanda ita ce ke kai sa wajen buga wasan. Haka kuma Mahaifin sa ya kan ba sa gafakar sa yayi amfani da ita wajen kara kwarewa a wasan na Chess.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng