Yayin da Ake Zarginsa da Sulalewa da Yahaya Bello, Gwamna Ya Roki Tinubu Alfarma
- Yayin da jihar Kogi ke fama da tarun matsaloli, gwamnan jihar ya nemi taimako daga Gwamnatin Tarayya domin dakile matsalolin
- Gwamna Usman Ododo ya bukaci taimakon ne inda ya ce jihar na neman taimako a ɓangaren rashin tsaro da kuma ambaliyar ruwa
- Hadimin gwamnan a bangaren yaɗa labarai, Isma'ila Isah shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma'a 19 ga watan Afrilu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi - Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi ya roki Gwamnatin Tarayya ta kawo masa ɗauki kan matsalolin da ya ke fama dasu.
Gwamnan ya nemi taimakon ne musamman ta bangaren rashin tsaro da kuma ambaliyar ruwa da suka addabi jihar, cewar Premium Times.
Wani roko gwamnan ya yi ga Tinubu?
Wannan na kunshe ne a cikin sata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Isma'il Isah ya fitar a jiya Juma'a 19 ga watan Afrilu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya yi wannan rokon ne yayin tarbar tawagar hukumar rarraba kudin shiga ta RMAFC a birnin Lokaja da ke jihar.
Ododo ya bukaci karin kudi daga hukumar domin dakile matsalolin da ke damun jihar, cewar jaridar Punch.
Gwamnan ya jero matsalolinsa ga Tinubu
"Jihar Kogi da ke makwabtaka da jihohi 10 Najeriya, ta na bukatar karin tallafi daga Gwamnatin Tarayya."
"Rashin tsaro da matsalar ambaliyar ruwa zai shafi sauran jihohi idan har ba a dakile su ba."
- Usman Ododo
Jihar Kogi a kwanakin nan ta na shan fama da hare-haren 'yan bindiga da suka kai munanan hare-hare musamman a yankunan karkara.
An bukaci tsige Gwamna Ododo a Kogi
A wani labarin, kun ji cewa wani fitaccen lauya a Najeriya, Deji Ajare ya bukaci Majalisar jihar Kogi ta fara shirin tsige Gwamna Usman Ododo.
Lauyan ya ce ya kamata Majalisar ta dauki mataki kan saɓa doka da gwamnan ya yi lokacin da hukumar EFCC ke shirin kama tsohon gwamna, Yahaya Bello.
Hakan ya biyo bayan sulalewa da Gwamna Ododo ya yi da mai gidansa, Yahaya Bello yayin da EFCC ke kokarin cafke shi.
Asali: Legit.ng