Malabu: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Tsohon Ministan Jonathan da Ake Zargi a Karkatar da $1.1bn

Malabu: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Tsohon Ministan Jonathan da Ake Zargi a Karkatar da $1.1bn

  • Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da tuhumar da hukumar EFCC ke yi wa Bello Adoke, tsohon ministan Jonathan
  • Hukumar EFCC na tuhumar Adoke ne da laifin zamba a cikin takaddamar lasisin neman mai (OPL) 245, wanda aka yi zambar $1.1bn
  • Alkalin kotun, Inyang Ekwo ya wanke Adoke sakamakon EFCC ba ta gabatar da kwararan hujjoji ba da suka alakanta Adole da zargin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa Bello Adoke, tsohon ministan shari'a a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Kotu ta wanke Bello Adoke daga zargin karkatar da $1.1bn
Malabu: Hukumar EFCC ta gaza alakanta ministan Jonathan da badakalar rashawar $1.1bn. Hoto: Trust Radio
Asali: UGC

Kotu ta wanke ministan Jonathan

Ana tuhumar Adoke ne da laifin zamba a cikin takaddamar lasisin neman mai (OPL) 245, wadda aka fi sani da badakalar cinikin mai na Malabu.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Hukumar NIS ta umarci jami'ai su sanya ido kan motsin tsohon gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin kotun, Inyang Ekwo, ya amince da bukatar da Mista Adoke ya shigar bayan da hukumar EFCC, ta kammala gabatar da jawabanta, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wanda ake tuhuma ne ya gabatar da bukata gaban kotun na ta yi watsi da karar hukumar EFCC ta shigar tare da wanke shi ba tare da ya gabatar da bayanan kare kai ba.

Adoke: EFCC ta gaza gabatar da hujjoji

Adoke ya gabatar da bukatar ne a kan cewa dukkanin shaidu da hujjoji da EFCC ta gabatar a karar, sun kasa alakanta shi da laifuffukan da ake tuhumarsa.

Talabin na TVCNews ya rahoto cewa mista Adoke yana fuskantar shari’a ne tare da Aliyu Abubakar, wani dan kasuwa, bisa zargin karkatar da kudade.

Ekwo ya yanke hukuncin a ranar Juma’a yana mai cewa EFCC ta gaza bayar da wasu kwararan hujjoji da ke alakanta Mista Adoke da laifin da ake zargin sa da aikatawa.

Kara karanta wannan

Wawure N80bn: EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamna da wasu mutum 3 a gaban kotu

Kotun da ta fara wanke Adoke

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa wata babbar kotun birnin tarayya da ke Jabi, Abuja ta wanke Bello Adoke daga zargin aikata laifin zamba.

Kotun a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris, ta kuma sallami wasu biyar da ake tuhuma a karar da hukumar EFCC ta shigar kan badakalar mai ta Malabu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.