Kotu ta wanke tsohon Ministan shari'a Bello daga zargin Hukumar EFCC

Kotu ta wanke tsohon Ministan shari'a Bello daga zargin Hukumar EFCC

- Kotu ta wanke Ministan shari’a na lokacin Jonathan watau Bello Adoke

- Mai shari’a Binta Nyako tace sam babu hujjar da za a iya kama Adoke

- Adoke yayi aikin da Shugaban kasa ya sa shi ne a ofis inji mai shari’ar

A makon nan labari ya zo mana cewa Ministan shari’a na kasar nan a lokacin tsohon Shugaban kasa Jonathan watau Mohammed Bello Adoke da ake zargi da saida rijiyoyin man Najeriya ba bisa ka’ida ba a 2011 yayi nasara a Kotu a Abuja.

Kotu ta wanke tsohon Ministan shari'a Bello daga zargin Hukumar EFCC
Ministan shari'an Jonathan ya kasa Gwamnatin Buhari a Kotu

Dama kun samu labari cewa Kotu ta bayyana cewa dalilin da zai sa a kama Ministan kasar saboda umarnin da ya bi a lokacin yana ofis. Kotu tace Ministan shari’ar kasar yayi aiki ne da umarnin da Shugaban kasa Jonathan ya ba shi.

KU KARANTA: Gwamnati ta bada umarni a duba lamarin da ya ja aka sungume sandar Majalisa

Babban Kotun Tarayya da ke Abuja a yanke hukuncin cewa Bello Adoke bai sabawa tsarin dokar kasa ba na yin abin da mai gidan sa ya nemi yayi. Mai shari’a Bello Nyako tace dokar kasa ta tanadi cewa Minista yayi biyayya ga Shugaban kasa.

A lokacin tsohon Shugaban kasa Jonathan an saida wani rijiyar man Najeriya na Malabu mai lamba na 245. Wannan magana dai har ta kai ana shari’a a Kasashen waje amma yanzu Kotu ta wanke Adoke daga hannun Hukumar EFCC tace bai yi sabo ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng