APC ko PDP: Malamin Addini Ya Fadi Jam'iyyar da Za Ta Lashe Zabukan Edo da Ondo
- Yayin da ake shirye gudanar da zabuka a jihohin Edo da Ondo, Fasto ya yi hasashen jam'iyyar da za ta yi nasara
- Fasto Elijah Ayodele ya yi hasashen ne inda ya tabbatar da cewa idan babu maguɗi, APC ce za ta lashe zabukan da za a yi
- Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben Edo a watan Satumba sai kuma na jihar Ondo a watan Nuwamba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Shugaban cocin Evangelical Spiritual, Fasto Elijah Ayodele ya yi hasashen abin da zai faru a zaben jihohin Edo da Ondo.
Faston ya yi hasashen ne bayan wakilin jaridar Punch ya yi masa tambaya a wata tattaunawa da suka yi.
Wane hasashe Faston ya yi a zabe?
Wannan hasashe na zuwa ne bayan hukumar INEC ta sanya watan Satumba domin zaben jihar Edo yayin da za a yi na jihar Ondo a Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ayodele ya ce akwai alamun cewa Gwamna mai ci a jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa shi ya ke da nasara a zaben.
"Abubuwa sun nuna cewa nasarar ta karkata ne ga gwamnan jihar Ondo mai ci yayin zaben fidda gwani."
"A zaben jihar Ondo, LP da PDP da kuma NNPP suna bata lokacinsu ne, APC ce za ta lashe zabe sai dai idan Ubangiji ya sauya lamarin."
- Fasto Ayodele
Harshen malamin kan zaben Edo
A zaben jihar Edo, Faston ya ce APC ce za ta lashe zaben cikin sauki wanda za a gudanar a watan Satumba.
"A zaben jihar Edo da ke zuwa, idan dai za a yi zabe ba tare da murdiya ba, APC ce za ta lashe zaben."
- Fasto Ayodele
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihohin Edo da Ondo.
Ganduje ya yi hasashen lashe zaben APC
Kun ji cewa Shugaban jam’iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje ya gargaɗi jam'iyyun adawa kan jihar Ondo.
Ganduje ya shaida musu cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da riƙe madafun ikon jihar a zaɓen gwamna da za a yi a watan Nuwamba.
Asali: Legit.ng