Matar Tsohon Gwamnan APC Ta Auri Kaninsa Bayan Ya Rasu? An Bankado Gaskiya

Matar Tsohon Gwamnan APC Ta Auri Kaninsa Bayan Ya Rasu? An Bankado Gaskiya

  • An yada jita-jitar cewa Betty Akeredolu, matar tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ta auri kaninsa bayan rasuwarsa
  • Wani shafin X ya wallafa cewa Betty za ta sake auren ne a ranar 6 ga watan Afrilu watanni hudu bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar
  • An yi bincike kan lamarin inda aka bankado cewa babu wani kamshin gaskiya kan labarin auren Betty da ake yadawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo – A kwanaki aka yi ta yada jita-jitar cewa Betty Akeredolu, matar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ta auri kaninsa bayan ya rasu.

Sai dai an binciko gaskiyar lamarin inda aka tabbatar da cewa babu kamshin gaskiya kan maganar auren.

Kara karanta wannan

Zaben fitar da gwani: An aike da saƙo mara daɗi ga Shugaba Tinubu kan gwamnan APC

An binciko gaskiya kan labarin cewa matar tsohon gwamnan APC ta auri kaninsa
An karyata jita-jitar cewa matar marigayi, Rotimi Akeredolu ta auri kaninsa bayan ya rasu. Hoto: Betty Anyanwu-Akeredolu.
Asali: Facebook

Jita-jita kan auren matar tsohon gwamna

Wani shafi a manhajar X mai suna @yabaleftonline ya wallafa cewa Betty Anyanwu za ta sake aure a ranar 6 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“An mika matar marigayin tsohon gwamnan jihar Ondo, Betty ga kaninsa, Farfesa Wole Akeredolu."

Sai dai bayan an wallafa labarin, The FackCheckingHub ta gudanar da bincike mai zurfi domin gano gaskiyar lamarin.

Yayin binciken, The FackCheckingHub ya tabbatar da cewa babu gaskiya kan cewa Betty ta auri kanin tsohon gwamnan.

Binciken ya kuma tabbatar da cewa an gudanar da wani biki ne na al’ada wanda ke haramta wa matar da mijinta ya mutu auren daya daga cikin 'yan uwansa.

Yaushe tsohon gwamnan ya rasu?

Betty dai ta auri tsohon gwamnan ne a watan Afrilun shekarar 1981 wanda ya rasu a ranar 27 ga watan Disambar 2023.

Kara karanta wannan

Tsohon dan takarar shugaban kasar Nijeriya, Ogbonnaya Onu ya rasu

Marigayin ya rasu ne a kasar Jamus ya na da shekaru 67 bayan ya sha fama da jinya mai tsawo.

Kafin rasuwar marigayin, Allah ya albarkaci rayuwar aurensu da ‘ya’ya hudu da kuma jikoki hudu.

Betty ta caccaki surukarta kan butulci

A baya, mun kawo muku labarin cewa Betty Anyanwu Akeredolu ta caccaki surukarta kan goyon bayan Gwamna Lucky Aiyedatiwa.

Betty wacce mijinta, Rotimi Akerdolu ya rasu a watan Disambar bara ta bayyana irin rashin adalci da Funke Akeredolu ta yi wa iyalansu.

Matar marigayin ta ce babu abin da mijinta bai yi wa Funke ba da ya ke raye amma yanzu ta watsa musu kasa a ido.

Asali: Legit.ng

Online view pixel