Dala a Babbar Riga: Hadimin Atiku Ya Dage, Yana So Hukumar EFCC Ta Binciki Ganduje
- Demola Rewaju yana so jami’an EFCC su maida hankali wajen binciken tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje
- Idan EFCC da gaske take yi wajen yakar rashin gaskiya, ya ce ta cafke Ganduje yadda aka kamo Cubana kwanakin baya
- A cewar Demola Rewaju, akwai bidiyo da za su iya daure shugaban na APC yadda EFCC ta damke fitaccen ‘dan kasuwar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Lagos - Demola Rewaju matashin ‘dan siyasa ne kuma ‘dan ga ni-kashe nin jam’iyyar PDP, ya yi kira ga hukumar EFCC ta kasa.
A yayin da yake tofa albarkacin bakinsa a dandalin X da aka fi sani da Twitter, ya bukaci a binciki Abdullahi Umar Ganduje.
'Bidiyon' Dala: EFCC da Abdullahi Ganduje
Demola Rewaju yana ganin idan da gaske ake so a yaki cin hanci da rashawa, ya zama dole a kama tsohon gwamnan Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin yana gwamna, an zargi Abdullahi Umar Ganduje da yawan karbar rashawa daga hannun ‘yan kwangila a jihar Kano.
Duk da jerin faya-fayen bidiyo da aka rika bankadowa a lokacin, ba a ji hukumar EFCC ta binciki Ganduje bayan barin ofis ba.
Ganduje: Kiran Demola Rewaju ga EFCC
"Idan da gaske take yi, ya kamata a ce tana taimakawa gwamnatin Kano wajen cafke shugaban APC, Abdullahi Ganduje kuma a gurfanar da shi."
"Hujjojin bidiyon Cubana yana jefa kudi daidai yake da hujjojin bidiyon Ganduje yana cusa daloli a cikin babbar riga."
- Demola Rewaju
EFCC za ta bi Ganduje kamar Cubana, Bobrisky?
Hadimin na Atiku Abubakar ya ce EFCC ta rabu da irinsu Cubana da Bobrisky, ta daina wata-wata, ta kama Dr. Abdullahi Ganduje.
‘Dan siyasar ya kawo misali da yadda EFCC ta tuhumi shugaban jam’iyyar PDP na kasa Tafa Balogun da laifi lokacin mulkin PDP.
Kamar yadda ya nuna a shafinsa, idan aka bi ta tashi, za a binciki Akinwumi Ambode.
"Idan a lokacin PDP, EFCC za ta iya kama shugaban jam’iyya kuma har a je kotu da Sufetan ‘yan sanda, EFCC a zamanin APC ta shirya yin abin da ya dace ga Najeriya."
- Demola Rewaju
Zargin cin hanci da rashawa a kwastam
Kwanaki kun ji labarin ana zargin wani jami’in kwastam ya soke cin hancin N1.1bn, an gano $31, 200 da N500, 000 a hannunsa
Binciken hukumar EFCC ya nuna akwai wani jami'i wanda ake zargin an ba cin hancin kusan N10bn a shekaru takwas.
Akwai hadimin wani babban ma’aikacin da ya maidowa EFCC N12m a cikin N126m da ake zargin ya wawura ta hanyar ofishinsa.
Asali: Legit.ng