Da Gaske Tsohon Gwamna Ya Rasu a Shekara 89? an Gano Gaskiyar Lamarin
- Yayin da ake ta yaɗa jita-jitar mutuwar tsohon gwamnan jihar Osun, Omololu Olunloyo ya yi martani kan lamarin
- Tsohon Gwamna ya karyata abin da ake yaɗawa na cewa ya mutu inda ya ce har yanzu ya na nan tukunna lokacinsa bai yi ba
- Wannan na zuwa ne bayan wasu kafafen sadarwa sun yada cewa dattijon mai shekaru 89 ya riga mu gidan gaskiya a kwanakin baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Tsohon gwamnan jihar Oyo, Dakta Omololu Olunloyo ya yi martani kan jita-jitar mutuwarsa.
Olunloyo ya ƙaryata cewa ya mutu kamar yadda ake yadawa inda ya ce ya na nan lafiya kalau.
Olunloyo: Wane martani tsohon gwamnan ya yi?
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne ga jaridar Punch a yau Juma'a 19 ga watan Afrilu a gidansa da ke Ibadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Omololu ya yi martanin ne yayin da wasu kafafen sadarwa suka yi ta yaɗa cewa ya mutu a kwanakin baya, cewar rahoton OsunDefender.
"Har yanzu ga ni nan a nan, ban tafi ba tukunna."
"Wadanda suke yada cewa mutum ya mutu, da masu hasashen, wata rana su ma za su mutu."
- Omololu Olunloyo
Olunloyo ya bayyana sa'ar da ya yi rayuwa
Omololu Olunloyo ya koka kan yadda mutane ke yawan yada mutuwar wasu inda ya tambaya ko shin su za su tabbata a duniya.?
Dattijon ya bayyana irin sa'ar da ya yi a rayuwa idan ya kwatanta da shekarun mahaifinsa, a cewar Oyo Affairs.
"Ni na yi sa'a a rayuwa, mahaifina ya mutu ya na da shekaru 42, mahaifiyata ta mutu da shekaru 102, gani ni kuma shekaruna 89 a yanzu, na wuce tsammanin shekarun da ake hasashe."
- Omololu Olunloyo
Yan bindiga sun hallaka basarake a Taraba
A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun hallaka fitaccen basarake a jihar Taraba da ke Arewacin Najeriya.
Marigayin da ke sarautar kauyen Sansani da ke karamar hukumar Gasol ya gamu da ajalinsa ne bayan maharan sun kutsa fadarsa tare da hallaka shi.
Lamarin ya faru ne a daren jiya Alhamis 18 ga watan Afrilu a kauyen yayin da lamarin ya jefa 'yan yankin a cikin fargana.
Asali: Legit.ng