Bayan Zargi, Gwamna Ya Dakatar da Kwamandan Jami'an Tsaron Sa Kai a Zamfara
- Yayin da ake zargin hukumar CPG da wuce gona da iri a aiki, gwamnatin jihar Zamfara ta ɗauki mataki kan kwamandan hukumar
- Gwamnatin ta sanar da dakatar da kwamandan hukumar, Kanal Rabi'u Garba duk ba ta bayyana dalilin daukar wannan matakin ba
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Abubakar Nakwada ya fitar a jiya Laraba 17 ga watan Afrilu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da kwamandan hukumar CPG a jihar, Kanal Rabi'u Garba mai ritaya.
Gwamnatin ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnati, Abubakar Nakwada ya fitar, cewar Punch.
Wane mataki gwamnatin Zamfara ta ɗauka?
Nakwada ya bayyana haka a jiya Laraba 17 ga watan Afrilu inda ya ce dakatarwar kwamandan hukumar CPG ta fara aiki nan take.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina mai sanar da ku cewa gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da kwamandan hukumar CPG a jihar, Kanal Rabi'u Garba mai ritaya."
"Wannan matakin na dakatarwar da aka yi ga kwamandan zai fara aiki nan take."
- Abubakar Nakwada
Sai dai sanarwar ba ta bayyana dalilin da ya sa gwamnatin jihar ta dakatar da kwamandan ba.
Zargin musabbabin dakatar da kwamandan CPG
Nigerian Voice ta tattaro cewa dakatarwar ba ta rasa nasaba da hirar da kwamandan ya yi a gidan rediyo.
Kwamandan yayin hirarsa a gidan rediyon Vision da aka wallafa a shafin Facebook inda ya zargi gwamnatin farada rashin taimakawa hukumar da kudi.
Kanal Rabi'u ya ce tun bayan kaddamar da hukumar a watan Janairu, gwamnatin ba ta ba su komai ba a kan abin ya shafi kayan gudanar da ayyukansu.
'Yan sa-kai da zargin kisa a Zamfara
A wani labarin, gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da cafke wasu 'yan sa-kai guda 10 kan zargin kisan malamin addinin Musulunci a jihar.
An zargin matasan 'yan sa-kai da kisan Sheikh Abubakar Hassan Mada a jihar inda suka yi masa kisan gilla.
An yi ta ta da jijiyoyin wuya kan zargin jami'an hukumar CPG inda gwamnatin jihar ta ce babu hannun jami'an hukumar a ciki.
Asali: Legit.ng