Gwamnatin Tinubu Ta Tura Buhunan Hatsi da Shinkafa Zuwa Jihar Arewa, Am Faɗi Abin da Za a Yi

Gwamnatin Tinubu Ta Tura Buhunan Hatsi da Shinkafa Zuwa Jihar Arewa, Am Faɗi Abin da Za a Yi

  • Gwamnatin tarayya karƙashin Bola Ahmed Tinubu ta ƙara tura buhunam hatsi da na shinkafa zuwa jihar Kwara
  • Kwamishinar sadarwa ta jihar, Bola Olukoju, ta tabbatar da cewa Kwara ta karɓi 12,058 na buhunan hatsi da buhunan shinkafa 8,700
  • Ministan noma da samar da isassen abinci a ƙasa, Abubakar Kyari ne zai kaddamar da fara rabon tallafin nan ba da daɗewa ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kwara - Gwamnatin jihar Kwara ta tabbatar da cewa ta karɓi sabon kaso na buhunan hatsi 12,058 daga Gwamnatin Tarayya karƙashin shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Buhunan da FG ta ƙara turawa zuwa jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiya sun haɗa da buhunan Masara, Gero da kuma Dawa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamman Arewa ya tsawaita hutun Ƙaramar Sallah a jiharsa, an gano muhimmin dalili 1

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq.
Kwara ta karbi ƙarin buhunan hatsi da shinkafa daga gwamnatin tarayya Hoto: AbdulRahman AbdulRazaq
Asali: Facebook

Buhunan hatsin sun ƙunshi 7,042 na buhunan Masara mai nauyin kilo 50, 2,916 na buhunan Gero mai nauyin kilo 50, da 2,100 na buhunan da Dawa mai nauyun kilo 50.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishiniyar sadarwa ta jihar, Misis Bola Olukoju ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu, 2024, Tribune Nigeria ta ruwaito.

Olukoju ta kara da cewa gwamnatin jihar Kwara ta kuma karbi buhunan shinkafa 8,700 masu nauyin kilo 25.

Za a kaddamar da rabon hatsi

Ta ce nan ba da dadewa ba ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari zai kaddamar da rabon hatsin a jihar.

Kwamishinar ta yi bayanin cewa a za a raba tallafin hatsin ga al'umma bisa tsarin da gwamnatin tarayya ta aiko da shi.

"Gwamnatin jihar Kwara ba ta yi ƙasa a guiwa ba ta ci gaba da tallafawa mutane domin shawo kan wahalar da ta biyo bayan cire tallafin man fetur," in ji kwamishinar.

Kara karanta wannan

Shugabanci: An faɗi wanda ya cancanci zama sabon shugaban jam'iyyar PDP daga Arewa

Idan baku manta ba Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin fitar da tan 42,000 na hatsi a rabawa ƴan Najeriya domin rage masu matsin da aka shiga a ƙasar.

Kwara ta karbi buhuna 12,058

A wani rahoton kuma Muhammed Inuwa Yahaya ya tsawaita hutun karamar sallah har zuwa ranar Jumu'a, 12 ga watan Afrilu, 2024 a jihar Gombe.

Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne domin bai wa mutanen jihar damar ci gaba da bukukuwan sallah ba tare da tunanin komai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel