InnalilLahi: 'Yan Mata Sun Kwanta Dama Yayin Mummunan Hatsarin Jirgi, an Ceto 3
- Wasu 'yan mata guda biyu sun ci karo da hatsarin jirgin ruwa a jihar Neja yayin kai ziyarar salla zuwa wurin 'yan uwa
- 'Yan matan biyu sun mutu nan take yayin da masu taimako suka tsamo gawarwakinsu daga cikin kogin
- Lamarin ya faru ne a kauyen Kofa da ke karamar hukumar Tafa a Neja a ranar Asabar 13 ga watan Afrilu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Neja - An shiga wani irin yanayi bayan wasu 'yan mata gida biyu sun mutu yayin da jirgin ruwa ya kife da su.
Lamarin ya faru ne a kauyen Kofa da ke karamar hukumar Tafa a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya.
Yaushe hatsarin jirgin ruwan ya faru?
Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru a ranar Asabar 13 ga watan Afrilu da yamma yayin da 'yan matan suka shiga jirgin domin ziyarar salla.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan mata sun dauki hayar jirgin ruwan ne tare da wasu mata guda biyu wadanda aka yi nasarar ceto su da direban jirgin ruwan.
Shugaban 'yan sa kai a yankin Tafa, Hussaini Abubakar ya tabbatar da cewa an kwashi wadanda aka ceto zuwa asibiti, cewar Punch.
Hussaini ya ce an yi kokarin ceto sauran 'yan matan da suka rasu amma ba a yi nasara ba yayin da aka yi nasarar ceto mutun uku ciki har da direban.
Yadda aka ceto sauran matan a kogi
Wani masunci a wurin, Abdul Gambo ya ce ya na gyaran jirgin ruwa a bakin kogi inda ya samu mummunan labarin.
"Na garzaya zuwa inda lamarin ya faru da jirgin ruwa tare da taimakon wasu jama'a."
"Mun yi nasarar ceto mutane uku da rai yayin daga bisani muka tsamo gawarwakin mutane biyu a cikin kogin."
- Abdul Gambo
Jaruman fina-finai sun mutu a kogi
A baya, mun kawo muku labarin cewa wasu jaruman fina-finan Nollywood hudu sun rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwa.
Jaruman hudu sun gamu da tsautsayin ne yayin zuwa daukar wani fim a jihar Anambra da ke Kudancin Najeriya.
Daga cikin wadanda suka mutun akwai jarumi Junior Pope wanda aka ceto shi da ransa kafin daga bisani ya ce ga garinku.
Asali: Legit.ng