Katsina: An Rufe Gidajen Mai 3 Bisa Zargin Saida Fetur ga Miyagun 'Yan Bindiga

Katsina: An Rufe Gidajen Mai 3 Bisa Zargin Saida Fetur ga Miyagun 'Yan Bindiga

  • Hukumomi a jihar Katsina sun rufe gidajen mai uku da ake zargin suna cinikayya da miyagun ƴan bindiga
  • Kwamitin kar-ta-kwana kan tsaro da inganta abincin jihar ya kuma kame wasu mutane goma da ake zargi da hannu cikin kasuwancin
  • Shugaban kwamitin, Jabiru Tsauri ya ce za su zurfafa bincike domin ɗaukar matakin shari'a kan waɗanda aka tabbatar suna da laifi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Katsina- Hukumomi a jihar Katsina sun garkame wasu gidajen mai uku bisa zargin sayarwa ƴan bindiga man fetur.

Kwamitin kar-ta-kwana kan tsaro da inganta abinci a jihar ya kuma cafke wasu mutane 10 da ake zargin suna da hannu cikin kasuwancin man fetur ɗin da ƴan bindigar.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yaran' Kwankwaso sun shiga gagarumar matsala kan dakatar da Ganduje

Channels tv ta ruwaito Shugaban Kwamitin, Jabiru Tsauri a yau Litinin ya ce an zurfafa bincike kafin ɗaukar mataki.

Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina
Gwamnatin Katsina ta rufe gidajen man ne bisa zargin sayarwa 'yan bindiga man fetur Hoto: Katsina State Government
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ana saidawa 'yan bindiga fetur da tsada"

Jabiru Tsauri, ya kara da cewa bayan laifin bawa 'yan ta'adda man fetur da ake zargin gidajen man da aikatawa, ana kuma tuhumarsu da sayar da man bisa farashi mai tsada.

Ya ce gidajen sun sayar da man sun sayar da litar mai a kan ₦733, ₦715 da kuma ₦730 wanda ya haura farashin da hukuma ta ƙayyade.

A kalamansa:

"Mun rufe dukkanin gidajen man, kuma waɗanda ake zargi da sayar da man a jarkoki sun shiga hannu inda za mu zurfafa bincike a kansu, idan an same su da laifi za a hukunta su kamar yadda doka ta tanada."

Tsauri ya ce bayanan sirrin da suka samu sun taimaka sosai wajen kai samame gidajen mai hudu a jihar, amma rahoton da ya bayar ya nuna uku daga ciki kawai aka rufe.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga ta ɓarke yayin da sojoji suka kashe bayin Allah da dama a Arewacin Najeriya

Jami'an tsaro sun daƙile harin ƴan ta'adda

Mun kawo muku rahoton yadda jami'an tsaro a jihar Katsina suka samu nasara wajen daƙile harin ƴan ta'adda.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq tabbatar da ƙwato muggan makamai a hannun ƴan bindigar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.