Yanzu Aka Fara: EFCC Ta Bankado Wasu Makudan Kudaden Tallafin Korona da Aka Sace a Mulkin Buhari
- Hukumar EFCC ta bayyana bankado wasu makudan kudade da ke da alaka da ayyukan jin kai a gwamnatin baya
- A lokacin mulkin Muhammadu Buhari ne gwamnatin Najeriya ta yi ayyukan rabawa jama’a kudi da sunan tallafi
- A halin da ake ciki, ana zargin wasu ma’aikatan gwamnati da cinye kudaden, lamarin da ya kai ga fara bincike mai zurfi
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
FCT, Abuja - Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) ta ce ta bamkado wasu makudan kudade da ke da alaka da tallafin Korona, lamunin Bankin Duniya da kuma kudaden da aka karbo na badakalar Abacha a ma’aikatar jin kai.
A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ce gwamnatin tarayya ta saki kudaden ga ma’aikatar domin aiwatar da ayyukan rage radadin talauci a fadin jihohi.
Idan baku manta ba, a zamanin Muhammadu Buhari ne gwamnatin Najeriya ta ware makudan kudade don rabawa gajiyayyu da sunan tallafin rage radadin talauci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu sun cinye kudin tallafin gwamnati
Sai dai, ana zargin kudaden da yawa sun shiga aljihun wasu daidaikun manyan gwamnati ne, lamarin da ya kai ga bincike mai zurfi, The Cable ta ruwaito.
A cewar EFCC bayan fara bincike:
“A farkon binciken, hukumar ta gayyaci tsoffi da jami’an ma’aikatar jin kai da aka dakatar kuma binciken da aka yi kan badakalar da aka yi a kansu an samu nasarar kwato N32.7billion da $445,000 zuwa yanzu.”
Yadda aka samo kudi aka ba ma’aikatar jin kai
Da hukumar ke bayyana gaskiyar inda aka samo kudin da kuma yadda gwamnati ta mika su ga ma’aikatar jin kai, Daily Post ta ruwaito EFCC na cewa:
“Bincike mai zurfi da EFCC ta yi ya bankado wasu ayyukan rashawa da suka hada da kudaden Covid-19, lamunin Bankin Duniya, kwatattun kudaden badakalar Abacha da Gwamnatin Tarayya ta saki wa ma’aikatar don aiwatar da aikinta na rage radadin talauci.
“Binciken ya kuma kai ga wasu jami’an ma’aikatar da aka kama da kuma dakatar da su da laifin almundahanar kudi.”
Batun tsohon gwamnan CBN da EFCC
A baya, kun ji yadda ake dambarwa tsakanin gwamnatin tarayya ta hannun EFCC na ci gaba da kai ruwa rana da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
A kwanan ne ne wata kotu a birnin Legas ta ba da belin Emefiele bisa wasu sharudda da kuma duba da dalilai masu muhimmanci.
Emefiele dai na hannun EFCC ne bisa zarginsa da aikata wasu laifukan da suke da alaka da cinye kudin kasa a karkashin kulawarsa.
Asali: Legit.ng