Bayan Rikici Kan Nadinsa, Basarake Ya Rasu Watanni Kadan da Karbar Sarauta
- An shiga jimami bayan rasuwar babban basarake a jihar Ondo, Julius Omomo watanni 11 da hawa sarautar Oda
- Marigayin ya rasu ne a jiya Asabar 13 ga watan Afrilu ya na da shekaru 83 bayan ya sha fama da jinya mai tsawo
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da iyalan marigayin suka fitar a yau Lahadi 14 ga watan Afrilu a jihar Ondo
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - An tafka babban rashi a jihar Ondo bayan rasuwar fitaccen basarake da ake kira Olojoda na Oda.
Marigayin mai suna Julius Omomo ya rasu ne ya na da shekaru 83 a duniya bayan ya sha fama da jinya.
Yaushe aka sanar da mutuwar basaken?
Wani daga cikin iyalan basaraken, Ade Adelakun shi ya bayyana mutuwar Sarkin a yau Lahadi 14 ga watan Afrilu, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adelakun ya ce Marigayin ya rasu ne a jiya Asabar 14 ga watan Afrilu bayan dadewa ya na jinya.
Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai kan-kan da kai da kuma tausayin al'umma, cewar rahoton Daily Post.
Ya kara da cewa a dan tsawon watannin da basaraken ya yi mulki, an samu ci gaba da kuma karin zaman lafiya.
Yaushe aka nada basaraken sarauta?
An zabi marigayin a matsayin sarki a ranar 30 ga watan Mayun 2023 yayin da aka nada shi a watan Disambar bara.
Sai dai nadin na shi ya ci karo da matsaloli inda wasu ke ganin an saba doka yayin zaban Omomo.
Daga bisani masu nadin sarautar sun tabbatar da cewa basu amince da Julius ba a matsayin sarkin Oda.
Basarake ya rasu bayan sallar idi
A baya, kun ji cewa An shiga jimami bayan rasuwar Osolo na masarautar Isolo a jihar Legas, Oba Kabiru Agbabiaka ya na da shekaru 64.
Basaraken ya rasu ne a ranar Laraba 10 ga watan Afrilu a Legas jim kadan bayan dawowa daga sallar idi.
Wannan na zuwa ne yayin da al'ummar Musulmai ke tsaka da gudanar da bikin sallar azumi a fadin Najeriya.
Asali: Legit.ng