Gaba da Gabanta: Jami’in Dan Sandan da Ya Yi Barazanar Sheke Farar Hula da Bindiga Ya Shiga Hannu
- 'Yan sanda sun kama dan uwansu da ya yi barazanar sheke farar hula da bindigarsa a jihar Edo da ke Kudancin Najeriya
- Rahoto ya bayyana yadda sabani ya kai ga cece-kuce tsakanin dan sanda da farar hula, lamarin da ya bata komai
- 'Yan sanda sun saba cin zarafin 'yan Najeriya, musamman a lamurran da suka shafi kan titunan kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Jihar Edo - Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta cafke wani jami’inta Prince Chima da laifin yiwa wani farar hula barazana da bindiga kirar AK-47 a garin Benin babban birnin jihar.
Lamarin ya faru ne a GRA da ke cikin garin Benin biyo bayan takaddamar da ta barke tsakanin jami’in da wani matashi, inda ake zargin matashin da cin mutuncin jami’in.
A cikin wani faifan bidiyo, an ga jami’in yana yiwa wasu mutane barazana a cikin gidansu da AK47 a lokacin da fahimtar junar ta tsananta, Pulse.ng ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kai ga kama jami'in
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor, ya ce bayan faruwar lamarin, kwamishinan 'yan sanda Funsho Adegboye, ya ba da umarnin kama jami’in tare da daukar mataki a kansa.
Ya ce kwamishinan, ya yi kira da a gudanar da bincike mai zurfi a kan lamarin, inda ya sa aka kama jami’in cikin gaggawa, rahoton Daily Trust.
Bayan kama jami'in, ya yi bayanin abinda ya hada shi da matashin da kuma yadda ta kaya a tsakaninsu har ta kai fada.
Kitirmurmura tsakanin jami'an tsaro da farar huka
Ba karon farko ba kenan da ake yada bidiyon yadda 'yan sanda ke cin zarafin fararen hula a Najeriya, hakan ya zama ruwan dare a kasar.
Sai dai, a lokuta mabambanta akan samu matakai da hukumar ke dauka kan jami'anta da aka kama da laifuka matukar akwai kwararan hujjoji.
Duk da haka, 'yan sanda a Najeriya sun saba da cin zarafin jama'a, inda suke tatsar kudi a hannayensu a kan tituna.
Yadda mawaki ya kaftawa dan sanda mari
A bangare guda, wani bidiyo ya yadu a kafar sada zumunta na yadda mawaki Seun Kuti ya kaftawa dan sandan Najeriya mari a jihar Legas.
Seun, wanda da ne ga fitaccen mawakin Fela ya fusata, inda aka ga yana fuskantar dan sanda tare ture shi da kirji har ta kai ya mare shi.
A wani sashe na bidiyon, dan sandan duk da hakurinsa da yadda ya yi shuru, mawakin ya kafta masa mari.
Asali: Legit.ng