Kano: Abba Kabir Ya Dauki Zafi Bayan Sakin 'Yan Daba Daga Kulle, Ya Sha Alwashi Kan Lamarin

Kano: Abba Kabir Ya Dauki Zafi Bayan Sakin 'Yan Daba Daga Kulle, Ya Sha Alwashi Kan Lamarin

  • Yayin da gwamnatin Kano ke kokarin dakile matsalar 'yan daba, Gwamna Abba Kabir ya fusata kan sakin wasu da aka yi
  • Gwamnan ya nuna bacin ransa inda ya ke zargin jam'iyyun adawa da hannu a sakin matasan bayan ya yi kokarin kawo karshen matsalar
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin ke kokarin dakile matsalar inda ta hana shirya fina-finai masu ɗauke da ayyukan 'yan daba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nuna bacin ransa kan yadda aka saki 'yan daba da ke kulle a jihar.

Gwamnan ya ce wannan wani mataki ne na kawo tsaiko a kokarin da gwamnati ke yi na dakile matsalar dabanci a jihar, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Fusatattun Yarbawa na son a raba Najeriya, sun farmaki sakateriyar gwamnati a Oyo

Abba Kabir ya sha alwashin kawo karshen 'yan daba a Kano
Gwamna Abba Kabir ya nuna bacin ransa kan sakin 'yan daba a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Su waye Abba ya zarga kan lamarin?

Abba Kabir ya bayyana haka ne yayin tarbar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana yawan 'yan dabar da aka kama domin yi musu hukunci amma abin takaici an sako su, cewar rahoton Newstral.

Har ila yau, gwamnan ya zargi jam'iyyun adawa da kokarin kubutar da 'yan dabar domin biyan buƙatar kansu ta siyasa.

Nasarar da Abba ya samu kan lamarin

"Lokacin da muka zo gidan gwamnati, mun samu matsalolin tsaro da dama da suka hada da kwacen waya da fashi da kuma dabanci."
"Yan daba na saran mutane domin kawai su karbi wayoyinsu, amma cikin ikon Allah mun kawo karshen matsalar cikin watanni 10 da kusan kaso 90."
"Abin takaici a karshen watan Ramadan, wasu matasa sun kutsa cikin masallaci a Dorayi tare da saran mutane da kuma sace wayoyinsu."

Kara karanta wannan

Watanni 2 da maganar komawa APC, Abba ya dauko binciken Ganduje da iyalinsa

- Abba Kabir

Matasa sun hallaka almajiri kan zargin kisa

A baya, mun kawo muku rahoton cewa wasu fusatattun matasa sun yi ajalin wani almajiri mai shekaru 16 a jihar Kano.

Matasan na zargin yaron da guntule kan wani Mohammed Sa'idu mai shekaru shida a duniya a ƙauyen Kanwa da ke karamar hukumar Madobi.

Dagacin garin, Yusuf Maitama ya ce matasan sun fi karfin jami'an tsaro inda suka kutsa kai cikin gidansa tare yin ajalin yaron nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.