An Shiga Jimami Yayin da Fitaccen Ɗan Jarida a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Shiga Jimami Yayin da Fitaccen Ɗan Jarida a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Shugabar gidan rediyon RadioNow 95.3FM, Kadaria Ahmed ta nuna alhini kan rasuwar ɗan jarida, Rotimi Sankore
  • Kadaria ta bayyana rasuwar marigayin ne a yau Asabar 13 ga watan Afrilu inda ta ce tabbas an tafka babban rashi
  • Ta bayyana marigayin a matsayin kwararre a fannin aikinsa inda ta ce tabbas za su yi kewar rashinsa sosai a ma'aikatar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Fitaccen dan jarida a Najeriya, Rotimi Sankore ya riga mu gidan gaskiya a Abuja a yau Asabar 13 ga watan Afrilu.

Shugabar gidan rediyon RadioNow 95.3FM, Kadaria Ahmed ita ta bayyana haka a shafin Facebook a yau Asabar 13 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Rai baƙon duniya: Jami'ar rundunar sojojin Najeriya ta yi babban rashi a birnin Abuja

An shiga jimami bayan dan jarida ya kwanta dama a Najeriya
Fitaccen dan jarida, Rotimi Sankore ya riga mu gidan gaskiya. Hoto: Rotimi Sankore.
Asali: Facebook

Mene silar mutuwar dan jaridar?

Kadaria ta bayyana marigayin a matsayin kwararre a aikinsa wanda ya ba da gudunmawa a harkar jarida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba mu samu cikakken bayani kan sukar rasuwar marigayin ba.

"Cikin alhini na ke sanar da ku cewa mun yi rashin kwararren ɗan jarida, Rotimi Sankore."
"Rotimi ya damu da matsalar Najeriya wanda hakan ya saka shi ya damu sosai domin ganin ya nemo mafita gare ta."
"Ayyukansa sun kawo sauyi matuka, tabbas mun yi babban rashi, ina mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da sauran 'yan uwa."

- Kadaria Ahmed

Gwagwarmaya da marigayin ya yi

Marigayin kafin rasuwarsa shi ne babban editan African Center for Development Journalism wanda ya ba da gudunmawa sosai a bangaren.

Har ila yau, Sankore ya rike editan Nigerian Info Group wanda ya kasance mai kula da jihohin Legas da Abuja da Kano da Ribas da kuma garin Onitsha.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun yi martani kan lafta masu haraji a wani titin jihar Legas da Calabar

Tsohon Ministan Buhari ya rasu

A baya, kun ji cewa tsohon ministan Muhammadu Buhari, Ogbonnaya Onu ya riga mu gidan gaskiya a jiya Juma'a 12 ga watan Afrilu.

Onu shi ne gwamnan jihar Abia na farko kafin daga bisani ya zama ministan kimiyya da fasaha a gwamnatin Buhari.

Shugaba Bola Tinubu da sauran manyan Najeriya sun tura sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin inda suka ce an tafka babban rashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.