Gwamnan Arewa Ya Ja Kunnen Malaman Musulunci Kan Siyasa, Ya Ba Su Shawara
- Yayin da aka kammala azumin watan Ramadan, Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya gargadi malaman addini kan siyasa
- Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda malaman suka mayar da mimbari wurin cimma burinsu da cin mutuncin shugabanni
- Nasir ya shawarce su da su janye daga irin wannan daɓi'a inda ya bukace su da su kare martabar shugabanni yayin wa'azinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kebbi - Gwamna Nasiru Idris na jihar Kebbi ya gargadi malaman addinin Musulunci kan shiga siyasa.
Gwamna Nasir ya shawarce su da su bar amfani da mimbari wurin cimma burinsu na siyasa, cewar Tribune.
Gargadi gwamna kan malaman Musulunci?
Gwamnan ya ce yin hakan ya sabawa kayarwar addinin Musulunci inda ya bukaci da su kare martabarsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamred Idris ya bayyana haka ne yayin tarbar Sarkin Gwandu, Alhaji Ilyasu Bashar wanda Wazirin Gwandu, Abdullahi Umar ya wakilce shi.
"A bayyane ya ke wasu malamai na amfani da mimbari wurin cin mutuncin 'yan siyasa ko kuma cimma burinsu na siyasa."
"Ni ma ban tsira daga hakan ba, ya kamata malamai su janye daga aikata hakan domin kare mutuncin shugabanni."
- Nasir Idris
Gwamna ya nuna rashin jin dadinsa
Ya bayyana rashin jin dadinsa kan irin wannan daɓi'a inda ya bukace su da su kaucewa haka domin daukaka addini da kuma mutunta shugabanni.
Gwamnan ya ce ya kamata malamai su kasancewar masu tarbiyantar da al'umma tare da kaucewa duk wani nau'in son zuciya, cewar Daily Post.
Wannan na zuwa ne bayan zargin wasu malaman da amfani da mimbari wurin aikata 'yan siyasa da kuma yabon wasu domin cimma burinsu.
Jaruma ta shiga matsala kan taba malami
A baya, mun ruwaito muku cewa kotu ta ci tarar jarumar fina-finan Nollywood, Halima Abubakar kan cin mutuncin fitaccen Fasto a Najeriya.
Halima ta batawa Faston mai suna Apostle Johnson Suleiman sun ne bayan ta wallafa karairayi a kansa a shafukan sada zumunta
Faston ya zargi jarumar da kokarin bata masa suna inda ta kira shi macuci kuma mayen mata wanda hakan ya sabawa dokar ƙasa.
Asali: Legit.ng