Ramadan: Babban Limami a Jihar Arewa Ya Rasa Kujerarsa Kan Rabon Kudi N500,000

Ramadan: Babban Limami a Jihar Arewa Ya Rasa Kujerarsa Kan Rabon Kudi N500,000

  • Yayin da Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya raba N500,000 ga limaman jihar, Alhaji Rufai Ibrahim ya yi murabus daga kujerar limanci
  • Alhaji Ibrahim shi ne babban limamin masallacin Wala da ke Birnin Kebbi wanda ya yi murabus kan rikicin da ya dabaibaye rabon kudin
  • Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da kwamishinan harkokin addinai a jihar, Muhammad Sani Aliyu kan lamarin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kebbi –Babban limamin masallacin Juma’a na Wala a Birnin Kebbi a jihar Kebbi, Alhaji Rufai Ibrahim ya yi murabus.

Limamin ya yi murabus din ne bayan samun rikici kan rabon N500,000 na Ramadan da Gwamna Nasir Idris ya yi ga limamai a jihar.

Kara karanta wannan

Jerin sabbin gwamnonin Arewa 7 da suka karbi bashin biliyoyi cikin watanni 6 kacal

Babban limami ya yi murabus kan rabon N500,000 na Ramadan
Gwamnatin Kebbi ta yi magana kan murabus din limamin masallaci kan rabon kudi N500,000 na Ramadan. Hoto: Nasir Idris.
Asali: Facebook

Musabbabin yin murabus din limamin a Kebbi

Kwamishinan harkokin addinai, Muhammad Sani Aliyu shi ya bayyana haka yayin hira da manema labarai a Birnin Kebbi, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sani Aliyu ya ce shugaban karamar hukumar Birnin Kebbi ya dakatar da Alhaji Ibrahim tun kafin ya yi murabus.

Ya ce murabus din limamain ya na da nasaba da cece-kuce da aka yi kan N500,000 inda ya ke zargin mataimakinsa, Malam Mamman Na Ta’ala ya ba shi N200,000 ne kacal.

Matakin da limamin ya dauka

Kwamishinan ya kara da cewa madadin limamin ya yi korafi ta hanyar ma’aikatar addinan jihar ko shugaban karamar hukuma sai ya wuce hukumar DSS.

“Bayan an dakatar da shi daga limanci, Alhaji Ibrahim ya ajiye aikin yayin da gwamnati ta karbi murabus din na shi tare da umartar mataimakinsa ya rike mukamin nasa a masallacin Juma’a.”

Kara karanta wannan

Rikicin El-Rufai da Uba Sani: Shehu Sani ya fadi gaskiyar lamari kan bashin Kaduna

Kwamishinan har ila yau, ya bukaci masarautar Gwandu ta nada sabon limami domin maye gurbin Alhaji Ibrahim, cewar PM News.

Gwamna ya raba kayan abinci a Kebbi

Kun ji cewa Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya raba kyautar kayan abinci har tirela 200 domin al’ummar jihar.

Gwamnan ya dauki matakin ne yayin da ake cikin wani irin mummunan hali na matsin tattalin arziki a fadin kasar baki daya.

Idris ya ce gwamnatinsa ta himmatu wurin ingata rayuwar ‘yan jihar ta bangarori da dama kamar yadda ya yi alkawari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel