Bayan Mutuwar Oba Lekan, Masu Nadin Sarauta Sun Sanar da Sabon Sarkin Ibadan
- Yayin da ake jimamin mutuwar Oba Lekan, majalisar nada sarki ta sanar da sabon sarkin kasar Ibadan wanda ake kira 'Olubadan'
- Mambobin majalisar sun amince da Oba Owolabi Olakulehin, a matsayin sabon Olubadan na masarautar Ibadanlan na 43
- Osi Balogun na Ibadanland, Oba Gbadamosi Adebimpe ne ya gabatar da sunan shi a matsayin wanda ya dace ya hau kan kujerar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ibadan, jihar Oyo - A yau Juma'a majalisar naɗa sarki ta zabi Oba Owolabi Olakulehin a matsayin sabon Sarkin Ibadanland wanda ake kira 'Olubadan' na 43
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa kujerar ta kasance babu sarki a kanta a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2024, bayan rasuwar Oba Lekan Balogun.
Oba Lekan Balogun ya yi sarauta na tsawon shekaru biyu kuma ya rasu yana da shekaru 81 a duniya. An nada shi sarki a ranar Laraba, 5 ga watan Janairu, 2022.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka zabi sabon sarkin Ibadan
'Yan majalisar sun amince su nada Oba Olakulehin a matsayin Olubadan a taron da Otun Olubadan na Ibadanland, Cif Rashidi Ladoja, ya kira a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Shafin Daily Post ya ruwaito Osi Balogun na Ibadanland, Oba Gbadamosi Adebimpe ne ya gabatar da sunan shi a matsayin wanda ya dace ya hau kan kujerar.
Ana sa ran za a aika sunan sa ga gwamnan jihar, Seyi Makinde, domin amincewa.
Matsayin Olakulehin a masarautar Ibadan
Oba Olakulehin shi ne babban basarake a layin wadanda za su iya gadar kujerar masarautar Olubadan daga bangaren Balogun, jaridar Leadership ta ruwaito.
Nadin ya kawo karshen cece-kuce da ake tafkawa a kan lafiyar Olubadan din mai jiran gado tun bayan da aka tsayar da shi takarar kujerar sarauta.
Sai dai an ruwaito cewa Otun Balogun na Ibadanland, Tajudeen Ajibola, bai halarci taron ba.
Gwamnan Anambra ya dakatar da Sarki
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnan jihar Anambra, Chukwuma C. Soludo ya dakatar da Sarkin Neni, Damian Ezeani saboda ya ba wani sanata mukamin sarautar gargaji.
Ifeanyi Ubah, sanata mai wakiltar Anambra ta Kudu ne aka yi wa nadin sarautar wanda ya saba da dokar masarautun jihar, kamar yadda sanarwar dakatarwar ta bayyana.
Asali: Legit.ng