Sunaye da hotunan manyan sarakuna 3 da suka mutu a jihar Oyo cikin watanni biyar

Sunaye da hotunan manyan sarakuna 3 da suka mutu a jihar Oyo cikin watanni biyar

Ba sabon labari bane cewa Alaafin na Oyo ya kwanta dama. Mutuwar Alaafin din na zuwa ne yan watanni bayan rasuwar wasu manyan sarakunan jihar Oyo guda biyu. Duk kamar an ruwa an dauke ne cikin kasa da watanni biyar.

Wanda ya fara amsa kira mahallicinsa cikinsu shine Olubadan na Ibadan, Oba Salihu Adetunji. Na gaba da ya mutu shine Soun na Ogbomosho, Jimoh Oyewumi.

Duk sun mutu ne a karkashin mulkin Gwamna Shehu Makinde na farko.

Ga jerin sarakunan da suka rasu

1. Olubadan na Ibadan

Sunaye da hotunan manyan sarakuna 3 da suka mutu a jihar Oyo cikin watanni biyar
Olubadan na Ibadan Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Oba Saliu Adetunji ya zama Olubadan na Ibadan, a watan Maris 2016. Yana da shekaru 88 a lokacin.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Sarkin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya kwanta dama

Ya yi mulki na tsawon shekaru shida. Ya rasu a ranar Lahadi, 2 ga watan Janairu yana da shekaru 93 a duniya.

2. Soun na Ogbomosho

Sunaye da hotunan manyan sarakuna 3 da suka mutu a jihar Oyo cikin watanni biyar
Soun na Ogbomosho Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Oba Jimoh Oladunni Oyewumi, Ajagungbade III, Soun na Ogbomoso a jihar Oyo ya rasu bayan shekaru 48 a kan kujerar sarauta.

‘Da ga Oba Bello Afolabi Oyewumi Ajagungbader II da Ayaba Seliat Olatundun Oyewumi ya hau karagar mulki a ranar 24 ga watan Oktoba, 1973.

Ya rasu a ranar 12 ga watan Disamban 2001.

3. Alaafin na Oyo

Sunaye da hotunan manyan sarakuna 3 da suka mutu a jihar Oyo cikin watanni biyar
Alaafin na Oyo Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, shine na baya-bayan nan a cikin sarakunan jihar da suka rasu a jihar.

Ya rasu yana da shekaru 83 kuma shine Alaafin mafi dadewa kan mulki, domin ya shafe tsawon shekaru 52 a kan kujerar.

Oba Lamidi, na uku daga gidan sarautar Alowodu, ya rasu a asibitin koyarwa na jami’ar Afe Babalola da ke Ado Ekiti a jihar Ekiti.

Kara karanta wannan

Mu muka kai harin Bam mashaya a jihar Taraba, Kungiyar ISWAP

Sarkin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya rigamu gidan gaskiya

Mun kawo a baya cewa Allah ya yiwa Sarkin Oyo, babban Sarki a kasar Yarbawa, Oba Lamidi Adeyemi, rasuwa.

Oba Adeyemi ya mutu ne da yammacin Juma'a a Asibitin koyarwa jami'ar Afe Babalola dake Ado Ekiti, rahoton Premium Times.

Cikin dare aka gaggauta kai gawarsa jihar Oyo domin fara shirin jana'izarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel