Hanyoyi 7 da lemu ke karawa mutun kyau

Hanyoyi 7 da lemu ke karawa mutun kyau

- Lemu yana da abubuwan kara kyau da dama ga fatar jikin dan adam wanda zakasokaji dadin jinsu

- Lemu yana kara hasken fata, farin hakora, magance kurajen fuska da kuma lafiyar farce

Hanyoyi 7 da lemun tsami zai iya sa ka kara kyau
Hanyoyi 7 da lemun tsami zai iya sa ka kara kyau

Lemu yana da abubuwan kara kyau da dama ga fatar jikin dan adam wanda zakasokaji dadin jinsu, abubuwan 7 sune:

1. Lemu yana kara hasken fata idan kana yawan amfani dashi saboda yana da sinadaran vitamin C da citric acid.

2. Lemu ana amfani dashi don kara hasken hakora idan aka hadashi da baking soda, idan aka sanya shi ga hakori da Q-tip aka sanya magogi aka goge hakoran.

3. Idan ka hada ruwan lemu da ruwan kwakwa, yana taimakawa wurin karawa fata haske.

4. Idan kana goga rabin lemu jikin gwiwar gannu kota kafa zai rage masu duhu yasa suyi haske.

5. Lemu yana zama a matsayin man shafawa idan ka hadashi da man ganyen shayi a cikin kofi shida na ruwa.

KU KARANTA KUMA: Manyan kurakurai 5 da maza ke tafkawa wajen neman aure

6. Lemu yana magance kurajen fuska. Abunda kawai zakayi shine ka shafa ruwan lemun a fuska.

7. Idan farcen ka ya bushe, ka hada man olive da ruwan lemu sai ka jika farcen a ciki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng