Jadawalin 2024: Jerin Jami’o’i 20 Mafi Daraja a Nijeriya
- Jami'ar Covenant ta sake rike kambunta karo na biyu na jami'a mafi daraja a Nijeriya bayan doke jami'ar Ibadan da jami'ar FUTA
- Times Higher Education, shafin da ke fitar da kididdigar jami'o'i mafi daraja a duniya ya sanar da hakan a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu
- Manyan jami'o'i 15 na Nijeriya sun fito ne daga Kudu maso Yamma, Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jami'ar Covenant ta doke jami'ar Ibadan da jami'ar fasaha ta tarayya, Akure, inda ta zamo jami'a mafi daraja a Najeriya a karo na biyu, bisa ga kididdigar Times Higher Education ta 2024.
"Jami'ar Covenant ce mafi daraja" - THE
Binciken da aka yi na baya-bayan nan da aka fitar a ranar Alhamis ya nuna cewa jami’ar Covenant da ke Ota, jihar Ogun, tana cikin manyan jami’o’i 1,000 a duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'ar da ke matsayi na 801 a duniya ta fara yin fice a shekarar 2018 bayan da ta samu lambar yabo ta jami'a mafi daraja a Najeriya, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
Jami'ar Ibadan ke bin bayan Covenant a matsayin jami'a ta biyu mafi daraja a kasar, yayin da jami'ar fasaha ta tarayya, Akure ta zo ta uku.
Yadda ake fitar da jadawalin jami'o'in
Rahoton shafin Times Higher Education na yanar gizo ya nuna cewa kididdigar jami'o'in duniya mafi daraja ta ƙunshi jami'o'i 1,904 daga cikin ƙasashe da yankuna 108.
Rahoton ya ce ana fitar da jadawalin jami'o'in ne ta hanyar la'akari da abubuwa biyar; koyarwa, yanayin muhalli na bincike, ingancin bincike, masana'antu da yadda duniya ke kallon jami'ar.
Jami'o'in Nijeriya daga Kudu da Arewa
Sauran jami'o'in da suka samu matsayi mafi girma a Najeriya sun hada da jami'ar Ilorin, jami'ar Nijeriya, Nsukka, jami'ar Afe Babalola da jami'ar Benin,
Jami'ar aikin gona ta tarayya, Abeokuta, jami'ar fasaha ta Ladoke Akintola, jami'ar jihar Legas, jami'ar Nnamdi Azikiwe, jami'ar Obafemi Awolowo, da jami'ar Fatakwal.
Daga cikin manyan jami'o'i 15 na Nijeriya, tara suna Kudu maso Yamma, biyu a Kudu maso Gabas, biyu a Kudu maso Kudu, daya a Arewa maso Yamma, daya kuma a Arewa ta Tsakiya.
Duba cikakken jerin a kasa:
- Jami'ar Covenant
- Jami'ar Ibadan
- Jami'ar fasaha ta tarayya, Akure
- Jami'ar Legas
- Jami'ar Bayero, Kano
- Jami'ar Ilorin
- Jami'ar Nijeriya
- Jami'ar Afe Babalola
- Jami'ar Benin
- Jami'ar noma, Abeokuta
- Jami'ar fasaha ta Ladoke Akintola
- Jami’ar jihar Legas
- Jami'ar Nnamdi Azikwe
- Jami'ar Obafemi Awolowo
- Jami'ar Fatakwal
- Jami'ar jihar Abia
- Jami'ar jihar Akwa Ibom
- Jami'ar taraya ta Alex Ekwueme
- Jami'ar Babcock
- Jami'ar Baze
Wuraren shakatawa 5 a Kaduna
A yayin da ake gudanar da bukukuwan karamar Sallah, Legit Hausa ta tattaro bayani kan wasu wuraren shakatawa biyar da ya kamata mutane su ziyarta a jihar Kaduna.
Mafi kyawun wurin taron jama'a domin nishadi, wasannin yara da kuma bude ido shi ne filin wasanni na Gamji, wanda ke tattare da dukkanin abubuwan debe kewa da ake bukata.
Asali: Legit.ng