Yan Bindiga Sun Kai Hari a Shingen Binciken ’Yan Sanda, Sun Tafka Babbar Barna
- Rundunar 'yan sanda a jihar Ebonyi ta sanar da cewa 'yan bindiga sun farmaki jami'ansu da ke bincike a Abakaliki, babban birnin jihar
- Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kuma kona motar ‘yan sanda da ke sintiri bayan kashe jami'i daya yayin harin
- Joshua Ukandu, kakakin rundunar ‘yan sandan Ebonyi, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis, mako biyu da kai irin wannan harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abakaliki, jihar Ebonyi - Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani jami’in dan sanda a wani hari da suka kai shingen bincike a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Joshua Ukandu, kakakin rundunar ‘yan sandan Ebonyi, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis.
Rundunar 'yan sanda ta magantu
Ya ce ‘yan bindigar sun kuma kona motar ‘yan sanda da ke sintiri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito Ukandu na cewa:
“An kai harin ne da sanyin safiyar Alhamis. Ina kan kokarin samun cikakken bayanin abin da ya faru, amma an kashe dan sanda guda, an kona mana mota.
"Za a samar da ƙarin bayani nan ba da jimawa ba."
Rahoton jaridar The Cable ya nuna cewa lamarin dai na zuwa ne makonni bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan tawagar ‘yan sanda da ke sintiri a jihar.
Harin 'yan bindiga kan 'yan sanda
‘Yan sanda hudu da wasu fararen hula biyu ne suka mutu a harin.
A ranar 2 ga watan Fabrairu, wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan tawagar ‘yan sanda da ke sintiri a kan hanyar Ngbo-Effium a karamar hukumar Ohaukwu ta jihar.
Daya daga cikin jami’an ‘yan sanda ya mutu a yayin arangamar inda daya kuma ya samu rauni.
Tsohon ministan Buhari ya rasu
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa tsohon ministan Buhari kan harkokin kimiyya da fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu ya rigamu gidan gaskiya.
An ruwaito cewa sau Onu ya rasu yana da shekaru 70 da doriya bayan shafe dogon lokaci yana da fama da rashin lafiya.
Onu shi ne gwamnan jihar Abia na farko bayan karbar mulki a Nijeriya, kuma ya nemi takarar shugaban kasa karkashin APC a zaben 2023.
Asali: Legit.ng