Ka Daina Sa Baki: Kungiyar Arewa Ta Ja Kunnen Kwankwaso Saboda Kalamansa

Ka Daina Sa Baki: Kungiyar Arewa Ta Ja Kunnen Kwankwaso Saboda Kalamansa

  • Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso, ya soki gwamnatin tarayya ne saboda gazawarta akan samar da tsaro
  • Kungiyar ta ce abin kunya ne a matsayinsa na tsohon ministan tsaro ya fito yana sukar gwamnati wanda shi ma bai tsinana komai ba a lokacinsa
  • Musayar yawun tazo ne a lokacin da rashin tsaro musamman sace-sacen mutane ya yawaita a yankin arewancin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gamayyar kungiyoyin matasan Arewa (CNYM) ta mayar da martani wa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, akan kalaman da yayi akan harkar tsaron Najeriya.

Rabi'u MUsa KWankwaso
Martanin kungiyar ya biyo bayan sukan da Kwankwaso ya yi akan harkokin tsaro ne inda ya bayyana gazawar gwamnatin tarayya. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso Asali: Facebook
Asali: Facebook

Kungiya ta yi wa Kwankwaso raddi

Martanin yazo ne biyo bayan sukan gwamnatin tarayya da yayi akan gazawarta na samar da tsaro a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Binciken Ganduje: Kungiya ta ja kunnen Abba Kabir, ta fadi babbar matsalarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar jiya, ta ce tsohon gwamnan jihar Kano ba shi da ikon yin katsalandan ga gwamnatin tarayya a kan harkokin tsaro.

Cikin martanin, shugaban kungiyar, Dr. Talba Isah, ya ce Kwankwaso da ya gaza a matsayin gwamna da ministan tsaro bai kamata ya sawa gwamnati baki ba a yanzu.

A cewar jaridar Leadership, kungiyar ta kara da cewa, martanin ya zama dole ne musamman a daidai lokacin da jam'iyyarsa ta kasa samar da kyakkyawan shugabanci a cikin watanni tara a jihar Kano.

Saboda haka kungiyar ta basa shawarar komawa jihar Kano ya tabbatar da mulkin adalci maimakon yin kalamai marasa amfani akan harkokin tsaron kasa.

Kwankwaso: Sanarwar da kungiyar ta fitar

A rahoton da jaridar Tribune ta fitar, ta ruwaito shugaban kungiyar yana cewa:

Kara karanta wannan

Yadda aka shiga tsakani don sulhunta Dr. Idris Dutsen Tanshi da abokan dambarwarsa

“Kungiyar hadin kan matasan Arewa ta ga bai dace Kwankwaso ya ce Tinubu ba zai iya magance matsalar rashin tsaro a kasar nan ba. Muna ganin wannan magana ta zama abin mayar da martani, musamman ma a daidai lokacin da dan takarar Kwankwaso, wanda ke rike da mukamin gwamna a jiha daya tilo da jam’iyyarsa ta yi nasara, bata iya samar da kyakkyawan shugabanci a cikin watanni tara da suka wuce ba."
“Saboda haka, idan har bai fara daukar matakan gyara ba, muna sanar da shi (Kwankwaso) cewa kungiyarmu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen samar da cikakken bayani kan yadda jihar Kano karkashinsa (Kwankwaso) da dan barandarsa, Abba Kabir Yusuf, suka yi wa tsaron kasa zagon kasa cikin watanni 9 da suka gabata."

Hanyar da za'a yaki 'yan bindiga

A wani rahoton, Kwankwaso ya bayyana cewa rundunar sojojin Najeriya za ta iya kawar da wannan matsala ta tsaro gaba ɗaya matuƙar ta samu kwarin guiwar da ya dace.

Ya ce duk da cewa hakkin gwamnatin tarayya ne kawo ƙarshen matsalar tsaro, ‘yan Najeriya na da muhimmiyar rawar da za su taka ta hanyar bada muhimman bayanai ga hukumomin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng