Gwamman Arewa Ya Tsawaita Hutun Ƙaramar Sallah a Jiharsa, An Gano Muhimmin Dalili 1
- Muhammed Inuwa Yahaya ya tsawaita hutun karamar sallah har zuwa ranar Jumu'a, 12 ga watan Afrilu, 2024 a jihar Gombe
- Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne domin bai wa mutanen jihar damar ci gaba da bukukuwan sallah ba tare da tunanin komai ba
- Ana ganin wannan ƙarin hutun ba zai rasa nasaba da hawan Sallah da aka saba yi a jihar Gombe har tsawon kwanaki uku ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Gombe - Yayin da al’ummar Musulmi ke bikin Ƙaramar Sallah, gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya amince da tsawaita hutu zuwa ranar Juma’a 12 ga Afrilu.
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Talata 9, Laraba 10 da Alhamis 11 ga watam Afrilu a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Sallah (Eid El Fitr), rahoton Channles tv.
Sai dai Gwamna Inuwa ya kara kwana daya a matsayin ranar da babu aiki domin jama’ar jihar su yi shagulgulan sallah cikin farin ciki, kamar yadda Leasdership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Gombe ne ya sanar da ƙarin hutun kwana ɗaya da gwamnan ya amince da shi a yammacin Laraba.
"An umurce ni da in sanar da ku cewa gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya (Dan Majen Gombe) ya amince da tsawaita hutun sallah.
Gwamnan ya tsawaita hutun zuwa Alhamis 11 ga Afrilu da Juma'a 12 ga Afrilu, 2024 domin bai wa ma'aikatan jihar damar ci gaba da shagalin Eid-el-Fitir na bana."
- in ji sanarwar.
Meyasa gwamna ya tsawaita hutun?
Tsawaita hutun ba zai rasa nasaba da yadda jihar Gombe ta saba gudanar da bukukuwan Sallah na kwanaki uku a jere ba.
Daga cikin shagulgulan da aka saba yi har da hawan doki wanda ake yi karkashin jagorancin mai martaba Sarkin Gombe, Abubakar Shehu Abubakar.
A ranar farƙo, ana yin Durbar (hawan Doki) wanda ake kira hawan Sallah jim ƙaɗan bayan idar da Sallar Idi.
Washe garin ranar sallah kuma ana yin hawan gidan gwamnati yayin da a rana ta uku kuma ake yin hawan Tudun Wada.
An fara samun tsaro a Katsina
A wani rahoton na daban Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana cewa alamu sun nuna Allah SWT ya karɓi addu'o'in neman zaman lafiya da mutane suka yi a Ramadan.
Jim kaɗan bayan kammala sallar idi a Katsina, Gwamna Dikko ya ce tsaro ya kara inganta a faɗin jihar cikin ƴan kwanakin nan.
Asali: Legit.ng