Mutane 2 Sun Fada Kogin Legas Bayan Mummunan Hatsarin Mota
- Hatsarin ya faru neyau Laraba da misalin karfe sha daya na safe akan gadar Third Mainland dake Legas
- Cikin wadanda lamarin ya ritsa da su, mutane biyu ne su afka cikin kogin bayan faruwar hatsarin yayinda da dama suka jikkata
- Jami'an agagin gaggawa sun ce sun dukufa wajen gudanar da bincike tare da ceto rayukan wandan da suka afka gadar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Lagos: An shiga jimami bayan hatsarin mota ya faru da misalin karfe sha daya na safe ne lokacin da al'ummar Musulmi ke cikin gudanar da bikin karamar sallah.
Lamarin ya faru ne yayin da ake tsaka da bukukuwan sallah karama a fadin Najeriya baki daya.
Yadda hatsarin ya afku a Legas
Hatsarin ya afku ne a kan gadar Third Mainland lokacin da birkin motar ya tsinke.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutum biyu cikin fasinjojin sun fada cikin kogin Legas yayin da aka garzaya babba asibitin Lagos Island da wadanda suka ji raunuka.
Ana kan gudanar da aikin ceto
Jami’an bayar da agajin gaggawa sun ce ‘yan sandan ruwa sun dukufa wajen jagorantar aikin ceto mutane biyun da suka fada ruwan.
Channels Television ya ruwaito Daraktaan ayyuka na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA), Olatunde Akinsanya yana cewa:
A yau (Ranar Laraba) da misalin karfe 11 na safe, anyi hadarin mota kusa da Adeniji Bypass. .
Wata motar bas mai dauke da fasinjoji 22 ta samu ballewar birki saboda tsananin gudu. Ana cikin haka ne sai ya yi karo da katangar da ke kan gadar Third Mainland sai kuma fasinja guda biyu suka nutse a cikin ruwan
Hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Legas din ta ce ta haɗa kai da ƴan sandan ruwa da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA, domin bincike da ceto wadanda suka fada ruwan.
Rahoton ya tabbatar da cewa al'ummar da suke wurin da hadarin ya afku sun taru domin bayar da taimako ga wadanda abin ya shafa.
Roka ta fada kogin Legas
A wani labarin kuma, roka ce dauke da yashi da mutane ta yi hadari a gadar Berger ta tsunduma cikin rafi a jihar Legas.
Mutane da dama sun bace sakamakon fadawa cikin rafin da motar ta yi daga saman gadar yayin da hukumomi suks dukufa wajen ceto rayuwarsu
Asali: Legit.ng