Da dumi-dumi: Roka rufta ta yi hadari ta fada rafi a Legas

Da dumi-dumi: Roka rufta ta yi hadari ta fada rafi a Legas

- Roka dauke da yashi da mutane ta yi hadari a gadar Berger ta tsinduma cikin rafi a jihar Legas

- Hadarin ya faru ne a daren ranar Juma'a 25 ga watan Satumban kamar yadda majiyoyi suka tabbatar

- Ma'aikatan hukumar agaji, 'yan sanda da direbobi suna can suna aikin ceto amma kawo yanzu ba a gano mutanen motar ba

Da dumi-dumi: Babban mota rufta cikin rafi a Legas
Da dumi-dumi: Babban mota rufta cikin rafi a Legas. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mutum 20 sun mutu a harin da ISWAP ta kai wa tawagar gwamnan Borno

Mutane da dama sun bace sakamakon fadawa cikin rafin Epe da wata mota ta yi daga gadar Berger a jihar Legas.

The Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Juma'a 25 ga watan Satumban 2020.

Hukumar Bada Agajin Gaggawa na jihar Legas ta tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Juma'a

Shugaban sashin hulda da jama'a na LASEMA, Nosa Okunbor ya ce ana can ana bincike da nufin ceto mutanen.

KU KARANTA: Hadiza El-Rufai na son mace ta gaji Sarkin Zazzau Shehu Idris

Ya ce, "Da isar su wurin da abin ya faru, sun gano cewa wata babbar mota mai taya shida makare da yashi ta fada cikin rafin.

"Ba a tabbatar da adadin mutanen da ke cikin motar ba a lokacin da hadarin ya faru.

"Tun safiyar yau, tawagar masu aikin ceto da suka hada da 'yan sanda da direbobi sun isa wurin suna ta kokarin ceto wadanda hadarin ya ritsa da su.

"Kawo yanzu ba a tabbatar da mutuwar kowa ba."

A wani labarin, FG ta gargadi dukkan ma'aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa sama da wadanda ke muhimman ayyuka su tabbatar sun zo aiki duk da yajin aikin da kungiyar kwadago ta sanar da fara yi a ranar Litinin.

Saboda annobar cutar korona, an shawarci wasu ma'aikatan gwamnatin su rika aiki daga gidajensu.

Kungiyoyin kwadago sun sanar da cewa za su fara yajin aikin ranar Litini a kan karin kudin lantarki da na man fetur.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164