An Shiga Tashin Hankali Bayan Jami'an NSCDC Sun Harbi Wata Mata a Filin Idi

An Shiga Tashin Hankali Bayan Jami'an NSCDC Sun Harbi Wata Mata a Filin Idi

  • An samu hargitsi a jihar Zamfara bayan an zargi jami'an hukumar NSCDC da harbin wata mata har lahira
  • Lamarin ya jawo wasu fusatattun mutane sun ƙona motar jami'an NSCDC ɗin bayan an zarge su da yin harbin
  • Sai dai, kakakin hukumar NSCDC a jihar ya musanta cewa jami'ansu ne suka yi harbin wanda ya yi sanadiyyar rasuwar matar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - An samu tashin hankali a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, yayin da jami’an hukumar tsaron farar hula (NSCDC) suka harbe wata mata a lokacin da suke ƙoƙarin bin ƴan daba.

Mummunan lamarin da ya auku a lokacin da Musulmai suka taru domin gudanar da Sallar Idi, ya haifar da tashin hankali, cewar rahoton tashar Channels.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki kan dan majalisa har cikin gida a jihar Arewa

Ana zargin jami'an NSCDC da hallaka wata mata
Ana zargin jami'an NSCDC da hallaka wata mata a Zamfara Hoto: @Official_NSCDC
Asali: Twitter

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa jami’an NSCDC a ƙoƙarin da suke na neman wasu ƴan daba ɗauke da muggan makamai, sun buɗe wuta lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wata mata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yin harbin ya jawo wasu fusatattun mutane sun ƙona wata motar jami'an NSCDC.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, kan lamarin inda ya ce jami’an NSCDC biyu da ke da alaƙa da harbin suna hannun ƴan sanda a halin yanzu.

Ya ce rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta fara gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.

A kalamansa:

"Akwai mutum biyu yanzu haka a hannunmu. Muna ci gaba da gudanar da bincike."

NSCDC ta musanta lamarin

Da aka tuntuɓi kakakin hukumar NSCDC a Jihar Zamfara, Ikor Oche, ya musanta zargin cewa jami’an hukumar ne suka harbi matar wacce ta rasu.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya fadi kokarin da zai yi a samu tsaro a jihar Zamfara

Ya ce jami’an suna wajen aikinsu ne domin lura da mutanen da suka fito zuwa Sallar Idi lokacin da suka ji ƙarar harbin.

A cewarsa, sun garzaya zuwa wurin inda suka tarar da wata mata da ta samu rauni.

A kalamansa:

"Saboda su ne kusa da wurin da lamarin ya faru, sai jama’a suka yo kansu. Sai da suka gudu domin tsira da ransu suka bar motarsu ta Hilux. Mutanen sun ƙona motar inda jami'anmu mutum bakwai suka samu raunuka. Ba su yi harbi ko kashe kowa ba."

NSCDC ta cafke fasto

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta cafke mutum uku da suka hada da wani fasto kan laifin sayar da takardun aiki na bogi ga wasu mutane.

Mataimakin babban kwamandan rundunar NSCDC, Ahmad Ahmad Gandi ya bayyana hakan a Lokoja a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng