Innalillahi: Babban Basarake Ya Rasu Jim Kadan Bayan Dawowa Daga Sallar Idi
- An shiga wani irin yanayi bayan samun labarin rasuwar babban basarake a jihar Legas, Oba Kabiru Agbabiaka
- Marigayin da ke sarautar Isolo a jihar ya rasu ne a yau Laraba 10 ga watan Afrilu bayan ya dawo daga sallar idi
- Shugaban karamar hukumar Isolo a jihar Legas, Olasoju Adebayo shi ya tabbatar rasuwar basaraken inda ya ce za a binne shi da yammacin yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - An shiga jimami bayan rasuwar Osolo na masarautar Isolo a jihar Legas, Oba Kabiru Agbabiaka ya na da shekaru 64.
Basaraken ya rasu ne a yau Laraba 10 ga watan Afrilu a Legas jim kadan bayan dawowa daga sallar idi, cewar rahoton Leadership.
Yaushe za a binne marigayin a Legas?
Shugaban karamar hukumar Isolo a jihar Legas, Olasoju Adebayo shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba 10 ga watan Afrilu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adebayo ya ce za a binne marigayin da misalin karfe 4 na yammacin yau kamar yadda addinin Musulunci ya koyar, cewar Vanguard.
Sanarwa kan mutuwar basaraken a Legas
"Na samu umarni daga mai girma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da na sanar da ku rasuwar basaraken Isolo, Oba Kabiru Agbabiaka."
"Basaraken ya rasu a yau Laraba 10 ga watan Afrilu ya na da shekaru 64 a duniya."
"Za a binne shi da misalin karfe 4 na yamma a yau a fadarsa da ke kan titin Akinbaye kamar yadda addinin Musulunci ya koyar."
"Muna masa addu'ar ubangji ya masa rahama ya kuma gafarta masa."
- Olasoju Adebayo
Tsohon alkalin kotun daukaka kara ya rasu
Kun ji cewa tsohon alƙalin kotun ɗaukaka ƙara, Ahmad Olanrewaju Belgore ya riga mu gidan gaskiya da shekaru 71 a duniya.
Kamaludden Gambari, shugaban kungiyar lauyoyi reshen jihar Kwara shi ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta a ranar Talata 9 ga watan Afrilu.
Marigayin ya yi ritaya a matsayin alƙalin kotun ɗaukaka ƙara a ranar 18 ga watan Afrilun 2023, bayan ya kai shekara 70.
Asali: Legit.ng