Yadda Aka Shiga Tsakani Don Sulhunta Dr. Idris Dutsen Tanshi da Abokan Dambarwarsa
- Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya nemi zaman sulhu tsakanin Malam Idris da wadanda yake takun saka da su
- Kwamishinan ƴan sandan jihar Bauchi ya bayyana matakan da zai dauka wajen ganin rikicin bai kara tashi ba
- Ya kuma jaddada cewa wajibi ne akan dukkan bangarorin su mutunta yarjejeniyar zaman lafiyar da suka sa wa hannu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Shahararren malamin addinin Musluncin, Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, ya yi hijira ne bayan rikici ya yi kamari tsakaninsa da gwamnatin Bauchi.
Rikicin ya kai ga a ranar 5 ga watan Fabrairun 2024, rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa ana nemansa ruwa a jallo bisa zargin rashin girmama kotu.
Malam ya dawo gida
Bayan malamin yayi gudun hijira, an nemi yin sulhu tsakaninsa da hukumomin jihar. Wanda hakan ya sanya shi dawowa gida Bauchi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, yana daga cikin wanda suka saka baki domin zaman sulhun.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Bauchi CP Auwal Musa Mohammad, ne ya jagoranci yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Malam Idris Abdulaziz da gwamnatin jihar Bauchi a hedikwatar 'yan sandan jihar.
Yarjejeniyar zaman lafiyan ta samu sa hannun daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), kwamandan hukumar tsaro ta NSCDC da kuma babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar Bauchi.
Yarjejeniyar dai ita ce yanzu ta bawa malamin damar sake dawowa gida ya cigaba da karantarwa ba tare da wani kalubale ba.
Bayanin kwamishinan ‘yan sanda
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya kuduri aniyar magance duk wani abin da zai kara kawo sabani tsakanin bangarorin ba tare da bata lokaci ba.
Ya kuma bayyana matukar godiyarsa ga maigirma gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad CON, bisa karrama kiran da Malam Nuhu Ribadu da sauran masu ruwa da tsaki suka yi akan yarjejeniyar zaman lafiyan.
Ya kuma ci gaba da cewa, dukkan bangarorin ya zama wajibi su cika sharuddan da ke cikin rubutaccen alkawarin da suka sanyawa hannu.
Kira ga Dr. Idris
A cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na Facebook, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar ya yi kira ga babban malamin yana mai cewa:
Ya kamata Malam Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya fahimci cewa duk da yake yana da ‘yancin fadin albarkacin baki, bai kamata ya rika amfani da mimbari wajen zagi ko yin kalaman batanci da cin mutuncin malamai ba.
Ya kara da cewa, ya kamata malamin ya yi kokari wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma ta hanyar wa’azinsa, ba tare da la’akari da bambancin ra’ayi ko addini ba.
Dr. Idris ya dawo gida
A wani rahoton kuma, daliban Dr. Idris Dutsen Tanshi sun ce ba gudu ba ja da baya wurin kira akan jaddada Tauhidi.
Jawabin na su yazo ne jim kaɗan bayan dawowar malamin nasu daga gudun hijira sakamakon sabanin da ya samu da gwamnati
Asali: Legit.ng