Gwamnan Arewa Ya Bi Sahun Tinubu, Ya Kara Ranakun Hutun Sallah a Jiharsa
- Gwamnatin jihar Katsina ta ayyana ranar Juma’a 12 ga Afrilu, 2024, a matsayin ranar hutu domin gudanar da bukukuwan ƙaramar Sallah
- Gwamnati ta umurci ma’aikata a Katsina da su yi amfani da wannan lokacin wajen yin addu'o'i ga shugabanni da samun zaman lafiya da ci gaban jihar da ƙasa baki ɗaya
- Ƙarin hutun a Katsina na zuwa ne duk da cewa gwamnatin tarayya ta tsawaita hutun ƙaramar Sallah zuwa ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya ayyana ranar Juma’a 12 ga watan Afrilu, 2024, a matsayin ranar hutu a jihar.
Gwamnan ya ayyana ranar ne a matsayin wacce ma'aikata ba su je wurin aiki ba domin bukukuwan ƙaramar Sallah.
A cewar Gwamna Radda, gwamnatinsa ta dauki wannan mataki ne domin ba ma’aikata a jihar damar cin gajiyar bikin Sallah tare da iyalansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Gwamna Radda ya ƙara hutun Sallah?
Matakin ayyana ranar a matsayin hutu ya biyo bayan matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na tsawaita hutun ƙaramar Sallah zuwa ranar Alhamis 11 ga watan Afrilun 2024.
A wata sanarwa a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu, kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar Katsina, Bala Zango, ya ambato Gwamna Radda na yi wa al’ummar jihar Katsina fatan yin bukukuwan Sallah lafiya.
An sanya sanarwar ne a shafin X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) na gwamnatin jihar Katsina.
Bugu da ƙari, gwamnan ya buƙaci mutanen jihar da su kasance masu lura da tsaro tare da yi wa jihar da Najeriya gaba daya addu’ar zaman lafiya a daidai lokacin da suke gudanar da bukukuwan Sallah na 2024.
An bada hutun Sallah
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata, 9 ga wata da ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun bikin ƙaramar Sallah.
Ministan harkokin cikin gida, Olabunmi Tunji-Ojo shi ne ya fitar da sanarwa kan hakan a madadin gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng