Sunnoni da ladduban ranan Idi 12 da yakamata Musulmi yayi la'akari da su

Sunnoni da ladduban ranan Idi 12 da yakamata Musulmi yayi la'akari da su

Yayinda mahajjata suka kammala hawan dutsen Arafah a yau Litinin, 9 ga watan Dhul Hijjah 1439, Musulmai a fadin duniya zasu yi shagalin Sallar Idi gobe Talata, 10 ga watan wanda yayi dai-dai da 21 ga watan Agusta, 2018.

Legit.ng Hausa ta kawo muku wasu sunnoni da suka tabbata daga Manzon Allah ﷺ yayin shirye-hiryen zuwa Sallar Idi gobe.

1-Yin ado da kwalliya dan ranar Idi. Hadisin Umar bin kaddhab ( Buhari 948)

2-Yin wankan ranar Idi kafin tafiya sallar idi. Abdullahi Ibn Umar R.A ya kasance baya fita sallar idi har sai yayi wankan idi (Muwatta Malik 384.

.Sa’id bn Musayyib Allah yayi masa Rahama yana cewa: ”Manyan sunnonin ranar Idi guda ukku ne tafiya masallacin idi a kasa da cin abinci kafin afita a idin karamar sallah da kamewa daga cin komai sai an dawo a babbar Sallah da yin wankan idi (Irwa’u galil)

3- Kame baki/ba’a cin koma sai an dawo daga Sallar Idi

4- Yin sallar Idi a musalla shine sunnah wato a bayan gari a wani fili ba masallaci ba saboda Manzon Allah ﷺ ya kasance yana fita musallane don yin sallar idi

5- Sunnane a fitar da mata da yara zuwa sallar idi,amma matan suyi shiga ta musulinci kuma kada su sanya turaren da kamshensa yake tashi. Sayyadina Abubakar R.A yana cewa: *”Hakkine akan kowace budurwa da macen aure fita zuwa sallar idi (Ibn Majah)

6- Tafiya masallacin idi kasa idan da ikon hakan saboda Manzon Allah s.a.w ya kasance yana tafiya masallacin idi a kasa kuma ya dawo a kasa. Aliyu bn Abi Dhalib R.A yana cewa: *”Yana cikin Sunnah tafiya sallar idi a kasa kuma aci wani abu kafin a fita idi (Tirmidhi)

KU KARANTA: Yan sanda sun damke matashin da yayi yunkurin kashe mahaifiyarsa

7- Canza hanyar dawowa ko hanyar zuwa masallacin idi. Manzon Allah s.a.w ya kasance yana chanza haryar dawowa daga masallacin idi kuma Ibn Umar R.A yana cewa: “Na koya daga Manzon Allah s.a.w chanza har dawowa daga masallacin idi”

*8- Yin kabarbari a ranar Idi. Ana fara kabbarar ne daga farkon wanta zul-Hijjah har zuwa karshen yini na ranar 13 ga wata anayi son yawaita yin kabbarori a kowane lokaci ba sai bayan sallah ba kadai

Imam San’ãni yana cewa:

Yin kabbar tun daren idi har zuwa faravsallar idi yin hakan sunnane abisa haduwa mafi yawan malamai saboda farrasa fadin

Sigan kabarbarin shine: Allahu akbar, Allahu akbar, La ilaha illa llah, Allahu Akba, Allahu akbar, wa lillahil hamd

9- Sanya Turare dan zuwa sallar idi* Abdillahi dan Umar R.A ya kasance baya fita sallar idi har sai yayi wanka ya sanya turare

10- Ba’a sallar nafila kafin sallar idi ko bayanta,kuma ba’a kiran sallah ko iqama

11 - Yin gaisuwar sallah da fatan Alkhairi da fatan Allah ya maimata mana*

12-.Cin wani abu daga cikin abinda ka yanka na layya bayan dawowa daga sallar Idi.

Manzon Allah SAW ya kasance baya cin abinci a idin babbar sallah har sai ya dawo daga Masallaci sannan yana fara cine daga wani sashe daga abinda ya yanka na layyarsa

A yi Sallah lafiya, Allah ya maimaita mana

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel