Ana Tsaka da Sallar Tahajjud, Matasa 5 Sun Yi Aika-aika a Masallacin Annur da Ke Abuja
- An tafka abin kunya bayan cafke wasu matasa da zargin satar waya lokacin sallar tahajjud a birnin Tarayya Abuja
- Rundunar 'yan sanda a birnin ta tabbatar da kama matasan guda biyar kan zargin sace waya kirar 'iPhone 13 pro' a masallacin Annur
- Yan sandan sun yi nasarar cafke matasan ne bayan korafin da suka samu daga Mohammed Bello cewar an sace masa waya a masallacin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Rundunar 'yan sanda a birnin Tarayya Abuja ta yi nasarar cafke matasa biyar kan satar waya a masallaci.
An cafke mutanen ne guda biyar bayan sace waya 'iPhone 13 pro' a masallacin Annur da ke Wuse II a Abuja yayin sallar tahajjud.
Yadda aka cafke matasan bayan sallar tahajjud
Kwamishinan 'yan sanda a birnin, Benneth Igweh shi ya bayyana haka a jiya Litinin ga watan Afrilu a Abuja, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Igweh ya ce an kama matasan ne bayan wani Mohammed Bello ya kai korafin cewa an sace masa waya yayin sallar tahajjud.
Ya ce daga bisani an yi nasarar gano wayar ta hanyar amfani da na'ura inda aka cafke matasan dauke da wayar.
Sunayen matasan da aka kama da sata
Kwamishinan ya ce an samu talabijin kirar 'Plasma' da mota kirar 'Mercedes Benz' da sauran kayayyaki masu amfani a wurin wadanda ake zargin.
Daga cikin matasan da aka cafken akwai Ibrahim Adamu da Muhammed Isah da Abdul Hussain, NewsTime ta tattaro labarin nan.
Sauran matasan guda biyu sun hada da Abdulgafar Sidi Mukhtar da kuma Muhammed Ya’u dukkansu a birnin Abuja.
Masu sallar tahajjud sun sha da kyar
A baya, mun ruwaito muku cewa wasu masallata sun tsira da kyar bayan babbar mota ta kubuce tare da kutsawa cikin masallaci.
Lamarin ya faru ne a karshen makon da ya wuce a jihar Neja jim kadan bayan kammala sallar tahajjud a masallacin.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa motar ta bugi bangaren mata da yara ne wandanda sun riga sun idar salla sun tafi kafin lamarin ya faru.
Asali: Legit.ng