An Kama Wasu Mutane 2 Kan Satar Janareton Masallaci a Kaduna

An Kama Wasu Mutane 2 Kan Satar Janareton Masallaci a Kaduna

  • Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta samu nasarar cafke wasu mutum biyu da ake zargi da sace janareton masallaci
  • Waɗanda ake zargin daou sun tafka wannan ta'asar ne a ƙaramar hukumar Hunkuyi ta jihar Kaduna
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mannir Hassan wanda ya tabbatar da cafke waɗanda ake zargin ya ce za a tura su zuwa kotu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da satar janareta da batir mai amfani da hasken rana a wani masallaci a Kaduna.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya bayyana hakan a ranar Asabar, 13 ga watan Janairu a Kaduna, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka bankawa fadar fitaccen basarake wuta a Najeriya

Yan sanda sun cafke barayin janareton masallaci
Yan sanda sun cafke barayin janareton masallaci a.Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Hassan ya ce bisa samun sahihan bayanai, jami’an tsaro a ranar Alhamis sun kama wanda ake zargin tare da kai shi ofishin ƴan sanda da ke unguwar Sabon Gari a ƙaramar hukumar Hunkuyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka cafke waɗanda ake zargin

A cewarsa:

"An kama wanda ake zargin ne saboda rashin yarda da yawon da yake a kusa da masallacin."

A cewarsa, yayin da ake yi masa tambayoyi, ya amsa laifin satar janareta da batir mai amfani da hasken rana a Hunkuyi da ƙauyen Nahuce a cikin masallatansu, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

A kalamansa:

"Wanda ake zargin ya ci gaba da cewa ya sayar da kayan da ya sata ga wanda ake zargi na biyu."
"An ƙwato wasu kayayyaki, kuma ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da wadlɗanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike."

Kara karanta wannan

Bayan kama 8, Asirin masu hannu a kisan bayin Allah sama da 150 ya ƙara tonuwa a arewa

Kotu Ta Tsare Matasa Masu Shaye-Shaye a Masallaci

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kotun shari'ar Musulunci dake zamanta a unguwar PRP a Gama cikin ƙaramar hukumar Nasarawa ta jihar Kano ta tsare wasu matasa kan zargin shaye-shaye a cikin masallaci a jihar.

Hakazalika, ana zargin matasan da ke Unguwar Rimin Kebe da buga wasan ludo a cikin masallacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel