CBN Ya Sake Daukar Mataki Na Karya Dala, ’Yan Canji Za Su Samu $10,000 Kan N1,101/$1
- Babban bankin Nijeriya (CBN) ya kuma ba 'yan canji $10,000 a kan farashin N1,101/$ bayan da ya kafa masu sharadi na siyarwa
- Bankin ya gargadi 'yan canjin cewa kada su siyar da $1 ta haura ribar kaso 1.5% na yadda ya ba su ita a farashin sari (N1,269/$)
- Wannan na daga cikin matakan da babban bankin ya dauka na ganin ya saita Naira domin ta yi daraja akan Dalar Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A karo na biyu, babban bankin Nijeriya ya sake sanar da sayar da daloli ga masu gudanar da harkokin canji na Bureau De Change.
Ya bayyana hakan ne a wata takardar sanarwa da aka wallafa a shafin bankin na yanar gizo a ranar Litinin, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
Sharadin da CBN ya kafawa 'yan canji
CBN ya ce ya shirya siyar da dala 10,000 ga kowanne dan canji a kan N1101/$ sannan ya umurci dillalan da su siyar da su a kan karin da bai wuce kashi 1.5 na farashin bankin ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A watan Maris ne babban bankin ya sayar wa 'yan canji dala 10,000 a kan kudi N1,251/$ sannan ya umarci su da su siyar wa kwastomomi a kan farashin da bai wuce N1,269/$1 ba.
Talabijin na AIT ya ruwato cewa wannan ya biyo bayan matakin da bankin ya dauka a baya na sayar da kudaden kasashen waje na dala 20,000 ga 'yan canjin da suka cancanta a fadin kasar a watan Fabrairu.
Sanarwar ta ce:
"Muna sanar da ku cewa CBN zai siyar da $10,000 ga BDCs a kan kudi 1,101/$. Sharadin shi ne za su sayar wa kwastomomi a kan farashin da bai wuce kashi 1.5 na farashin bankin ba."
'Yan canji sun nemi sassauci daga CBN
Wannan na zuwa bayan roko da kungiyar 'yan canji ta Najeriya ta yi wa bankin na ya rage farashin Dala da ya ke ba mambobinta zuwa kasa da N1,251/$.
Shugaban ABCON na kasa, Aminu Gwadabe ne ya bayyana haka a cikin wata wasika da ya aike wa daraktan sashen kasuwanci da musayar kudi na CBN, wadda jaridar PUNCH ta samu.
CBN ne ya bayyana cewa an samu raguwar kudaden da ake samu daga kasashen waje a Najeriya da kusan dala biliyan 1.02 a cikin kwanaki 18, ya zuwa ranar 4 ga Afrilu.
Emefiele ya gurfana gaban kotu
A safiyar yau Litinin Legit Hausa ta ruwaito cewa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya gurfana gaban babbar kotun jihar Legas da ke ikeja kan zargin aikata laifuffuka 26.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Emefiele gaban kotun bayan da ta sake samun wasu hujjoji da ke nuna yadda ya karkatar da wasu biliyoyin kudaden kasar waje da kuma karbar rashawa.
Asali: Legit.ng