Rundunar Sojoji Ta Dauki Mataki Kan 'Yan Ta'addan da Suka Farmaki Jami'anta a Borno
- Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da hallaka ƴan ta'adda shida da suka farmaki jami'anta a jihar Borno
- Ƴan ta'addan sun yi wa sojojin kwanton ɓauna ne inda suka hallaka Laftanar ɗaya tare da raunata wasu sojoji huɗu
- Biyo bayan aukuwar lamarin an aika da ƙarin jami'ai inda suka yi artabu da ƴan ta'addan tare da fatattakarsu daga maɓoyarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa ta kashe ƴan ta’adda shida da suka kashe jami’anta a hanyar Biu-Buni-Yadi, a jihar Borno.
Ƴan ta'addan dai sun farmaki jami'an sojojin ne bayan sun yi musu kwanton ɓauna a kan hanyar.
Rundunar ta ce bayan aukuwar lamarin, an aika da ƙarin sojoji inda suka tarwatsa maɓoyar ƴan ta'addan a cikin Timbuktu Triangle, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me rundunar sojoji ta ce kan lamarin?
Daraktan yaɗa labarai na rundunar, Edward Buba, shi ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, inda ya ce Laftanar guda ɗaya kawai aka kashe a yayin kwanton ɓaunan.
Manjo-Janar Buba, ya ce sauran sojoji huɗu da suka samu raunuka, ana ci gaba da ba su magani a asibiti, rahoton jaridar PM News ya tabbatar.
A kalamansa:
“A ranar 5 ga watan Afrilu da misalin ƙarfe 09:35 na safe, dakarun Operation Hadin Kai, sun fuskanci kwanton ɓauna na ƴan ta'adda a hanyar Buratai-Buni-Yadi.
"Abin baƙin ciki, a yayin fafatawar an kashe Laftanar guda ɗaya. Yayin da wasu sojoji huɗu suka samu raunuka inda ake duba lafiyarsu a asibiti.
"Dakarun sojojin da aka ƙara aikawa sun bi ƴan ta’addan har zuwa maɓoyarsu a cikin Timbuktu Triangle tare da yin musayar wuta."
"Sojojin sun yi nasarar kashe shida daga cikin ƴan ta’addan tare da ƙwato bindigu ƙirar AK 47 guda biyar da harsashi na musamman mai kaurin 7.62mm guda 103."
- Janar Edward Buba
Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka tantiran ƴan ta'adda guda uku a jihar Kaduna.
Sojojin sun sheƙe ƴan ta'addan ne bayan sun yi musu kwanton ɓauna lokacin da suke kan hanyar kai gyaran baburansu.
Asali: Legit.ng