“Bamu Hana Ka Murabus Ba”: Kungiyar Kwadago Ta Fusata, Ta Tura Sako Mai Zafi Ga Peter Obi
- Kungiyar kwadago ta sha alwashin tsige shugaban jam'iyyar Labour kan wasu dalilai masu karfi da suka gindayo
- NLC ta ce Peter Obi na da zabin barin jam'iyyar Labour, hakan ba zai zamewa jam'iyyar wani kalubale ba a gaba
- Ana tunanin sake ba Peter Obi tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2027 da a yanzu 'yan siyasar Najeriya ke shiryawa
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Najeriya - Kungiyar kwadago ta Najeriya ta shaida wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour cewa yana da ’yancin barin jam'iyyar ba wanda zai hana shi.
Kakakin kungiyar NLC, Benson Upah ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi dashi ranar Lahadi.
Shugabannin NLC sun sha alwashin cewa, ba za su huta ba har sai sun tsige Julius Abure a matsayin shugaban jam'iyyar Labour ta kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bamu amince da shugabancin Abure ba, NLC
Upah ya ce duk da zaben da aka yi ‘ba bisa ka’ida’ da ya mayar da Abure kan mukaminsa, kungiyar ba za ta yi mubaya'a ga shugabancinsa ba.
A tattaunawarsa da jaridar Punch, ya ce:
“Matsayinmu kan wannan lamari a fili yake kuma bai canza ba. Har yanzu bamu san Abure ba. Ba batun tsigewa bane, a iya saninmu, babu shi.”
A halin da ake ciki kuma, kungiyar ma’aikatan da suka yi ritaya a karkashin kungiyar ma’aikata ta Legas, sun bukaci shugaban jam’iyyar na kasa kuma shugaban NLC, Joe Ajaero, da ya yi murabus saboda takaddamar shugabancin da ke gudana.
Rikicin jam'iyyar Labour da Peter Obi
Obi dai ya sha rikici tsakaninsa da shugabannin jam’iyyar Labour kan yadda ta gudanar da taron gangamin jam'iyyar a Nnewi da ke jihar Anambra, duk da rokon da ya yi na neman karin shawarwari.
Tsohon gwamnan na Anambra, a wata tattauna ta shafin X Space a ranar Juma'ar da ta gabata, ya bayyana takaicinsa kan abubuwan da ke faruwa.
Obi ya ce bai halarci taron gangamin Labour da ya samar da Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa ba saboda shugabannin jam’iyyar sun kasa gamsuwa da yawon neman goyon baya da yake.
Peter Obi ya tunzura 'yan jam'iyyar Labour
Kalamansa dai sun rura wutar rade-radin da aka yi a baya cewa mai yiwuwa dan takarar shugaban kasar na 2023 ya fara hangen barin jam'iyyar nan ba da jimawa ba.
Sai dai, a nasa bangaren, Upah ya bayyana cewa, babu wanda ya hana Peter barin jam'iyyar, kuma tsayuwarsa a ciki ba zai kare ta da komai ba.
A zaben da ya gabata na shugaban kasa, jam'iyyar labour ce ta zo na uku, a lokacin da Peter Obi ke rike da tutarta a 2023.
Peter Obi jam'iyyar za ta kara ba tikiti a 2027
A wani labarin kuma, kun ji yadda jam'iyyar Labour ta yi taro, inda ta bayyana aniyarta na kuma ba Peter Obi tikiti a 2027.
Wannan na zuwa ne bayan da Obi ya sha kaye a zaben da aka gudanar na 2023 a watan Faburairun shekarar da ta gabata.
A halin da ake ciki, Peter Obi da wani yanki na jam'iyyar Labour na ci gaba da kai ruwa rana kan wasu matsaloli.
Asali: Legit.ng