Fargaba Yayin da Shugaban Jam’iyyar Adawa Ya Sha da Kyar Bayan Wuta Ta Lakume Gidansa

Fargaba Yayin da Shugaban Jam’iyyar Adawa Ya Sha da Kyar Bayan Wuta Ta Lakume Gidansa

  • An shiga fargaba yayin da shugaban jam'iyyar LP, Julius Abure ya sha da kyar bayan gobara ta kama gidansa a Abuja
  • Gobatar ta fara ne da misalin karfe daya na daren ranar Laraba a gidansa da ke Abuja inda ya tsira da kyar daga iftila'in
  • Sakataren jam'iyyar, Obiorah Ifoh shi ya tabbatar da haka inda ya ce an yi yunkurin ganin bayan shugaban jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jam'iyyar LP a Najeriya ta bayyana yadda shugabanta ya sha da kyar yayin da wuta ta kama gidansa a Abuja.

Sakataren jam'iyyar, Obiora Ifoh ya ce Julius Abure ya tsallake rijiya ta baya bayan wutar ta kama da tsakar daren yau Laraba 3 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Abuja: Mummunar gobara ta tashi a gidan shugaban karamar hukuma

Gidan shugaban jam'iyyar adawa a Najeriya ya kama da wuta
Shugaban jam'iyyar LP ya tsira da kyar bayan wuta ta kama gidansa. Hoto: Julius Abure.
Asali: Facebook

Yadda wutar ta kama a gidan Abure

Ifoh ya ce an garzaya da Abure da iyalansa wani asibiti mai zaman kansa bayan tsira da kyar daga iftila'in, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shugaban jam'iyyar LP ta kasa, Julius Abure da safiyar yau Laraba ya sha da kyar yayin da aka yi niyyar hallaka shi a gidansa da ke Abuja."
"Gidansa ya kama da wuta da misalin karfe daya na dare yayin da ya ke bacci tare da iyalansa."
"Dukkan iyalan Abure sun tsinci kansu cikin iftila'in inda ya yi matukar ba su wahala a kokarinsu na tsira da rayukansu."

- Obiorah Ifoh

Jami'an kashe gobara sun ba da gudunmawa

Wani daga cikin iyalan Abure ya bayyana cewa kawai tashi suka yi suka ga gidan na ci da wuta inda makwabta suka tayar da su daga bacci.

TheCable ta tattaro cewa sai da jami'an tsaro a yankin suka balla kofofin gidan da tagogi kafin samun tseratar da su.

Kara karanta wannan

APC ta dauki zafi kan sharrin da aka yi wa Matawalle, ta gargadi PDP a Zamfara

Har ila yau, jami'an kashe gobara sun samu isowa inda lamarin ya faru yayin da suka taimakawa shugaban jam'iyyar LP da iyalansa suka tsira.

Obiorah ya kara da cewa an kwashi Abure da iyalansa zuwa wani asibiti mai zaman kansa domin ba su kulawa.

An kama shugaban jam'iyyar LP

Kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta cafke shugaban jam'iyyar adawa a Najeriya ta , Julius Abure a birnin Tarayya Abuja.

Ana zargin Abure da badakalar makudan kudi da suka kai N3bn mallakin jam'iyyar ta adawa a Najeriya da sauran korafe-korafe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel