Mafita Mafi Sauki: Reno Omokri Ya Ba ’Yan Najeriya Shawarin Yadda Za Su Shawo Kan Karyewar Naira
- Tsohon hadimin shugaban kasa Reno Omokri ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika siyan kayayyaki da ake samarwa a kasar
- Omokri ya yi wannan kiran ne yayin da ya kara jaddada cewa Naira ta tsaya a kasa da N1300 kan kowacce dala a kan farashin canji, sabanin rade-radin cewa za ta kai N2000
- Daga nan ne ya bayyana wasu kayayyaki da kamfanonin d aya kamata 'yan Najeriya su koma amfani da su sosai a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon Shugaba Jonatha, ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika ba da muhimmanci ga amfani da kayayyakin Najeriya don ci gaba da dorewar darajar Naira idan a kasuwar canji.
Reno ya ci gaba da cewa ta haka ne kadai za a iya rage yawaitar faduwar darajar Naira zuwa Dala, inda ya ce ya zuwa ranar 5 ga watan Afrilu, farashin dala ga Naira Naira ya tsaya ne N1300 sabanin rade-radin da ake yi na cewa farashin zai haura N2000 nan kusa.
Omokri, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a, 5 ga watan Afrilu, ya yabawa kansa da sauran ke kira ga da'awar #GrowNairaBuyNaija a yanayin da ake ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin fara gangami don siyan kaya da Naira
Wannan gangami na siyan kayayyaki da Naira dai su Reno sun fara shi ne don karya gwiwar masu hasashen darajar kudin Najeriya zai yi kasa zuwa N2000 kan kowacce dala.
Daga nan sai ya yi kira ga wadanda har yanzu suke taskance dala a lalitarsu da fatan cewa nan ba da dadewa ba za ta tashi da su sake tunani, inda ya ce hakan ne mafi alheri a gare su.
Ya kuma ci gaba da cewa dala za ta kara faduwa a lokacin da matatun Dangote da na Fatakwal suka fara siyarwa da kuma raba mai ga jama'a a Najeriya.
Wasu kayayyaki na Najeriya kowa zai iya siya?
- Ku yi kira tare da Glo
- Ku hau mota kirar Innoson ko Nord
- Ku yi gini simintin Dangote da BUA
- Ku yi karin kumallo da kanzon Nasco
- Abincin rana da abincin dare kuma ku ci shinkafar gida
- Ku dafa jollof da tumatirin Erisco
- Ku yi firar masoya a Tantalisers da wurare masu balangu da tsire
- Ku sha Zobo
- Ku yi shagulgulan biki da barasar gida ta kwakwa
- Ku hau jirgin Air Peace a madadin Air France, KLM, ko Lufthansa
- Ku yi siyayya a kasuwannin gida
- Ku ci burodin rogo a madadin burodin alkamar waje
- Ku kalli Enyimba da Kano Pillars
- Ku kalli fina-finan Nollywood a Silverbird
- Ku saurari wakokin Najeriya
- Ku sanya sutura irin aso oke, agbada, babanriga, ko isi agu
Bobrisky ya ci zarafin Naira
Ana tsaka da jin yadda za a farfado da darajar Naira, fitaccen mai siffanta kansa da mata, Bobrsiky ya wulanta kudin a Najeriya.
An ruwaito cewa, EFCC ta kame shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin cin zarfin kudin kasar.
Ba wannan ne karon farko da ake kama 'yan Najeriya da laifin cin zarafin kudi ba, hakan kan faru a lokuta mabambanta.
Asali: Legit.ng