Karin Kudin Wuta: Kano da Sauran Jihohi 12 da Suka Shirya Inganta Wuta Ga Al'ummarsu
Yayin da ake ta korafin karin kudin wutar lantarki a Najeriya, wasu jihohi sun shirya ba da ingantacciyar wuta ga alummarsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Hakan ya biyo karin kudin wutar da kusan kaso 200 musamman ga wadanda ke rukunin Band A a Najeriya.
Wasu 'yan Najeriya na ganin cewa hakan zai inganta wutar a kasar ganin yadda ake shan fama da matsalar, cewar Thisday.
Jihohin da suka sha alwashin inganta wuta
Legit Hausa ta jero muku jihohin da suka shirya ba da ingantacciyar wuta a jihohinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Kano
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana himmatuwarta wurin ba da ingantacciyar wutar ga kamfanoni da al'ummar jihar, cewar Punch.
Daraktan yada labaran gwamnan, Sunusi Dawakin Tofa ya ce gwamnati ta fara aikin inganta wutar a Challawa Goje Tiga shekaru 10 da suka wuce inda ya ce an ci karfin aikin da kaso 90.
2. Nasarawa
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta yi haɗaka da masu ruwa da tsari a harkar domin samar da wutar a jihar.
Manajan hukumar zuba hannun jari a jihar ta IDA, Ibrahim Abdullahi ya ce sun yi hadakar ce domin inganta tattalin arzikin jihar.
3. Benue
Gwamnatin jihar Benue ta ce shirye-shirye sun kankama domin samar da babban kamfanin rarraba wutar a jihar.
Kwamishinan makamashi, Omale Omale shi ya tabbatar da haka inda ya ce sun kawo tsare-tsare domin inganta wutar a jihar, cewar rahoton Eagles FM.
4. Legas
Kwamishinan yada labarai a jihar, Gbenga Omotosho ya ce Legas ta na kan gaba wurin tabbatar da samar da wutar a jihar.
Jihar Legas na daya daga cikin jihohin Najeriya da suke fama da matsalar wutar lantarki duk da bunkasar tattalin arziki da suke da shi.
5. Ekiti
Kwamishinan yada labarai a jihar Ekiti, Taiwo Olatunbosun ya ce sun jima da samar da ingantacciyar wuta a jiharsu wanda ke zaman kanta.
Sauran jihohin sun hada da Kaduna da Kebbi da Zamfara da Sokoto da Ondo da Osun da Oyo da kuma Enugu, cewar TheCable.
NERC ta yi karin bayani kan kudin wuya
Kun ji cewa bayan ƙarin kudin wutar lantarki a Najeriya, hukumar NERC ta yi karin haske kan korafe-korafe da ake yi.
Hukumar ta fitar da sanarwa bayan cece-kuce da ake yi kan karin kudin wutar inda ta fayyace wadanda abin ya shafa.
Hakan ya biyo bayan ƙarin kudin wutar da hukumar ta yi da kaso 200 musamman ga wadanda suke rukunin Band A a fadin ƙasar.
Asali: Legit.ng