Mutane 9 Sun Rasu, 30 Sun Jikkata a Turereniyar Karbar Kayan Sallah Na Tsohon Gwamnan APC

Mutane 9 Sun Rasu, 30 Sun Jikkata a Turereniyar Karbar Kayan Sallah Na Tsohon Gwamnan APC

  • An shiga fargaba bayan mutuwar mutane tara yayin karbar kyautar salla a gidan Sanata Aliyu Wamakko a jihar Sokoto
  • Wani jami'in hukumar tsaro ta NSCDC ya tabbatar da mutuwar mutane tara yayin da ya ce fiye da 30 sun samun raunuka
  • Jam'iyyar PDP a jihar ta yi Allah wadai da wannan abin takaici inda ta bukaci jami'an tsaro su kaddamar da bincike kan lamarin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Jami'yyar PDP a jihar Sokoto ta bukaci jami'an tsaro su yi bincike kan cunkoso da aka samu a gidan Sanata Aliyu Wamakko.

Wanna na zuwa ne bayan tabbatar da mutuwar mutane tara da raunata akalla 30 yayin turereniyar karbar kayan Sallah.

Kara karanta wannan

Adadin mutanen da aka kashe a harin Kogi ya karu, an roki Tinubu ya dauki mataki

An rasa rayuka a gidan tsohon gwamnan APC yayin karbar kayan salla
Mutane 9 sun mutu a turereniyar karbar kayan salla a gidan Sanata Aliyu Wamakko. Hoto: Senator Aliyu Magatakarda Wamakko.
Asali: Facebook

PDP ta yi Allah wadai da faruwar lamarin

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jami'yyar, Hassan Sahabi Sanyinnawal ya fitar, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanyinnawal ya ce lamarin ya faru yayin cunkoson karbar kayan salla a gidan tsohon gwamnan jihar a Sokoto.

"Mun samu labarin abin takaicin da ya faru a gidan Sanata Aliyu Wamakko kan turereniya da ya yi sanadin rasa rayuka."
"Muna tura sakon jaje kan wannan lamari ga iyalan wadanda suka mutu tare da addu'ar samun sauki ga wadanda suka samu raunuka."

PDP ta bukaci gudanar da bincike

- Hassan Sahabi

"Saboda haka muna kira ga jami'an tsaro da su kaddamar da bincike kan wannan lamari domin dakile faruwar hakan nan gaba."

- Hassan Sahabi Sanyinnawal

Jam'iyya har ila yau, ta bukaci da a biya diyya ga wadanda suka rasa rayukansu dalilin turereniyar a gidan Sanata da ke wakiltar Sokoto ta Arewa, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Masallata sun sha da kyar a sallar tahajjud, mota ta kutsa masallaci a jihar Arewa

Mutane sun mutu a karbar Zakka a Bauchi

A baya, mun baku labarin cewa akalla mutane bakwai ne suka mutu yayin turereniyar karbar Zakka a jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya.

Lamarin ya faru ne a kan hanyar Jos yayin da mai gidan man AYM Shafa ke raba zakkar 10,000 ga mata yayin da ake cikin watan azumin Ramadan.

Rundunar 'yan sanda a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin wanda ya yi sanadin mutuwar matan inda ta saki sunayensu .

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.