PDP da APC Sun Gaza, Kwankwaso Ya Fadi Jam'iyyar da Za ta yi wa Yan Najeriya Adalci

PDP da APC Sun Gaza, Kwankwaso Ya Fadi Jam'iyyar da Za ta yi wa Yan Najeriya Adalci

  • Jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yanzu jam'iyyarsu ce kadai za ta iya magance matsalolin da Nijeriya ke fuskanta
  • Yayin da yake nuna gazawar jam'iyyar PDP da APC mai mulki a kasar, Kwankwaso ya ce NNPP na da tsari na saita al'amuran kasar
  • Hakazalika, tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce sojojin Nijeriya ne kaɗai za su iya kawo karshen 'yan bindiga ba wai jihohi ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sanata Rabi’u Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP 2023, ya ce jam’iyyarsu tana da tsarin da za ta bi wajen magance kalubalen da kasar ke fuskanta.

Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan shugabanci da tsaro a Nijeriya
Kwankwaso ya ce jam'iyyar APC da PDP sun gaza wajen jagorantar jama'a. Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Facebook

Jam'iyyar PDP da APC sun gaza?

Kara karanta wannan

NERC ta tsokano ‘yan kwadago, ana yi wa Tinubu barazana saboda kudin lantarki

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto Kwankwaso, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron kwamitin zartarwa na NNPP a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, NNPP ita ce mafita daya tilo ga ‘yan Nijeriya, inda ya ce jam’iyyar APC da PDP sun gaza wajen jagorantar jama’a.

Da yake magana kan rashin tsaro a kasar, Kwankwaso, wanda tsohon ministan tsaro ne, ya ce sojoji na da karfin kawo karshen 'yan bindiga idan aka ba su kwarin guiwa.

Kwankwaso ya magantu kan tsaro

Ya ce duk da cewa hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnatin tarayya ta magance matsalar tsaro, ‘yan Najeriya ma na da muhimmiyar rawar da za su taka.

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, jagoran NNPP ya ce:

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya soki wasu gwamnoni, ya faɗi hanya 1 da za a kawar da ƴan bindiga a Najeriya

“Mun ga jihohi suna kafa wasu jami'an tsaro. Wani lokaci sai dai kayi dariya. Matsayin da yake a yau, sojan Nijeriya ne kawai zai iya yaki da 'yan ta'adda.
“Wasu daga cikin mu daga kauyuka muka fito, a yanzu mutanenmu ba sa iya yin noma saboda matsalar tsaro. Muna kallo 'yan bindiga suna cin zarafin 'yayanmu."

Za a binciki Ganduje a Kano

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamiti da zai binciku shekaru takwas na mulkin Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce kwamitin zai gano yadda tsohuwar gwamnati ta karkatar da kadarorin jihar, da kuma rashawar sama da biliyan 1 da ake yi wa Ganduje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.