'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 19 a Wani Sabon Hari a Jihar Arewa

'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 19 a Wani Sabon Hari a Jihar Arewa

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai sabon harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Omala ta jihar Kogi
  • A yayin farmakin wanda suka kai a ƙaiyen Agojeju Odo, tsagerun sun hallaka mutum 19 tare da ƙona gidaje masu yawa
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya bayyana cewa an tura ƙarin jami'an tsaro zuwa yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai farmaki garin Agojeju Odo da ke ƙaramar hukumar Omala a jihar Kogi.

Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai sun kashe mutum 19 tare da ƙona gidaje da dama, cewar rahoton tashar Channels.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin farmaki kan bayin Allah a watan azumi, sun kashe mutane da yawa

'Yan bindiga sun kai hari a Kogi
'Yan bindiga sun hallaka mutum 19 a jihar Kogi Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kogi, William Aya, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma'a, 5 ga watan Afirilun 2024, rahoton jaridar The Punch ta tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

William ya bayyana cewa ƴan bindigan waɗanda ba a san ko su wanene ba, sun kai harin ne a ranar Alhamis.

Aya ya ce ofishin ƴan sanda na ƙaramar hukumar ya sanar da shi cewa mutum 19 ne suka mutu yayin da wasu suka samu raunuka a harin.

Ya bayyana cewa kwamishinan ƴan sandan jihar Kogi, CP Bethrand Onuoha, ya tura ƙarin ƴan sanda zuwa garin, inda ya bada tabbacin cewa za’a cafke waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.

An yi kira ga gwamnati

A halin da ake ciki, mazauna yankin sun ce ƴan bindigar sun kai hari a garin Agojeju Odo, yayin da ƙauyukan da ke makwabtaka da su kamar Ajokpachi Odo, Bagaji duk a ƙaramar hukumar Omala a halin yanzu babu kowa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke matasa masu yunkurin kona sansanin 'yan gudun hijira a jihar Arewa

Al’ummomin sun yi kira ga gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo, da jami’an tsaro da su kawo musu ɗauki ta hanyar tura ƙarin jami’an tsaro yankin, domin maharan sun fi ƙarfin ƴan sandan da ke yankin.

Ƴan bindiga sun kai hari a Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga hanyar Kuta da ke Minna babban birnin jihar Neja, inda suka far wa mutanen da ke zuwa sallar Tahajjud.

Mummunan lamarin dai ya faru ne lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare a lokacin da Musulamai ke fitowa yin sallar dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng