Zargin Rashawa: Ganduje Ya Magantu Kan Binciken da Gwamnatin Kano Za Ta Yi Masa
- Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya caccaki Gwamna Abba Kabir Yusuf kan kafa kwamitin da zai binciki gwamnatinsa
- Ganduje ya ce babu wata tuhuma ko bita da kulli da za ta bata masa suna ko na iyalansa kasancewar babu wani laifi da ya aikata
- Shugaban jam'iyyar APC na yanzu, ya kuma zargi Gwamna Yusuf da gaza aiwatar da ayyukan azo a gani a Kano tun hawansa mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya caccaki Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ka kafa kwamitoci da za su bincike shi da iyalinsa.
Gwamnatin Kano za ta binciki Ganuduje
Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamna Yusuf a ranar Alhamis ta kaddamar da kwamitocin shari'a da za su binciki zargin rashawa da karkatar da kadarorin gwamnatin a mulkin Ganduje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan jihar ya ce sun shigar da karar tsohon gwamnan kan zargin karbar rashawar $413,000 da kuma Naira biliyan 1.38.
Mai shari'a Faruk Lawan ne aka ba jagorancin kwamitin da zai binciko yadda tsohuwar gwamnati ta karkatar da kadarori daga 2015 zuwa 2023.
Ganduje ya yi wa Abba martani
Sai dai a ranar Juma'a ne jaridar Daily Trust ta rahoto Ganduje ya yi martani kan kwamitin da aka kafa, inda ya zargi gwamnan da yunkurin bata masa suna da kuma yi wa iyalinsa bi ta da kulli.
Ganduje wanda ya yia magana ta bakin kakakinsa, Edwin Olufu ya ce:
"Babu wasu ayyukan azo a gani da gwamnan ya yi duk da cewa jihohi sun samu karin kudade daga asusun kasafi na kasa.
"Idanunsu sun rufe wajen ganin sun bata sunana da na iyali na, sun manta da cewar akwai doka a dukkan abubuwan da ake yi."
"Abba na yi mani bita da kulli" - Ganduje
Jaridar Vanguard ta rahoto Ganduje ya zargi gwamnan Kano da cewa ya manta hukuncin babbar kotun Kano na cewa Antoni Janar na tarayya da hukumar EFCC ce kadai za ta iya tuhumar Ganduje.
"A maimakon su tsaya suna yi mani bi ta da kulli da bata mani suna, zai fi su mayar da hankali wajen bunkasa rayuwar al'umar jihar Kano.
"Har yanzu suna da damar da za su iya zuwa in ba su kundin tsarin tafiyar da mulki da na yi amfani da shi, wannan ne kaɗai hanyar kawo ci gaba a jihar Kano."
- A cewar sanarwar.
Ganduje ya kuma jaddada cewa ya mulki jihar Kano ne da zuciya daya kuma bai taba boye komai na yadda ya tafiyar da mulkinsa ba, don haka ba zai ji tsoron komai ba.
Ganduje ya garzaya babbar kotu
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito maku ce Abdullahi Umar Ganduje ya nemi babbar kotun Kano da ta dakatar da gwamnatin Kano daga tuhumar karbar rashawa a lokacin da yake gwamna.
Tun biyo bayan wani faifan bidiyo da aka nuna wani da aka yi ikirarin Ganduje ne yana karbar daloli, tsohon gwamnan ke fuskantar tuhumar rashawa daga gwamnatin Kano.
Asali: Legit.ng