Gwamna Uba Sani Ya Yi Muhimman Nade-Nade 5 a Gwamnatinsa

Gwamna Uba Sani Ya Yi Muhimman Nade-Nade 5 a Gwamnatinsa

  • Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya sanar da yin sababbin naɗe-naɗe har guda biyar a gwamnatinsa
  • Gwamnan ya naɗa sabon shugaban hukumar kula da harkokin majalisar dokokin jihar da wasu muƙamai guda huɗu
  • Sakataren yaɗa labaran gwamnan wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ya ce naɗin na su zai fara aiki ne nan take

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya yi sabbin naɗe-naɗen muƙamai a gwamnatinsa.

Naɗe-naɗen a cewarsa ya yi su ne bisa ƙoƙarin da ya ke ci gaba da yi na ganin gwamnatinsa ta yi aiki yadda ya dace, cewar rahoton jaridar Leadership.

Uba Sani ya yi sababbin nade-nade
Gwamna Uba Sani ya raba mukamai a Kaduna Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Gwamnan a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa Muhammad Shehu ya fitar, ya tabbatar da yin naɗe-naɗen na mutum biyar.

Kara karanta wannan

Takaddamar El-Rufai da Uba Sani: Jam'iyyar APC ta fadi wanda take goyon baya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wanene Uba Sani ya ba muƙamai?

Gwamnan ya naɗa Honorabul Nuhu Goroh-Shadalafiya a matsayin shugaban hukumar kula da harkokin majalisar dokokin jihar Kaduna, har zuwa lokacin da majalisar za ta amince da naɗin.

Sauran waɗanda aka nada sun haɗa da Ahmed Abdullahi Maiyaki, manajan daraktan hukumar yaɗa labarai ta jihar Kaduna (KSMC), Ibrahim Abdulkarim Adamu, manajan daraktan hukumar raya kasuwanni Kaduna.

Sauran waɗanda suka samu muƙamim sun haɗa da Idris Aminu, manajan daraktan kamfanin samar da wutar lantarki na jihar Kaduna da Mista Bamai Abu Nehamiah, babban mataimaki na musamman kan Tsaro.

Dalilin da ya sa aka naɗa su

Sanarwar ta ce, naɗin nasu ya biyo bayan ayyukan da suka yi a baya da kuma jajircewarsu wajen yi wa jihar Kaduna hidima, rahoton Politics Nigeria ya tabbatar.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Sokoto ta ciyo bashin makudan kudi? Gwamna Ahmed ya fayyace gaskiya

"Waɗannan naɗe-naɗe masu muhimmanci sun nuna ƙudirin gwamnati na yin amfani da masu basira da sababbin tunani don ciyar da jihar Kaduna gaba."

Yayin da yake taya su murnar naɗin da aka yi musu, Gwamna Sani ya buƙace su da su kasance masu himma tare da sanya dabaru da tsare-tsare masu inganci don ciyar da jihar gaba.

Gwamna Uba Sani ya kuma yi musu fatan Allah ya ba su ikon gudanar da ayyukansu yadda ya dace. Naɗe-naɗen na su dai za su fara aiki ne nan take.

APC ta goyi bayan Uba Sani

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta nuna goyon bayanta kan Gwamna Uba Sani, saboda bayyana bashin da ya gada wajen Nasir El-Rufai.

Jam'iyyar ta yi nuni da cewa matakin da gwamnan ya ɗauka na faɗin halin da jihar ta ke ciki abin a yaba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng