Gwamnati Ta Fadi Dalilin Kara Kudin Wutar Lantarki Zuwa N225/KwH Ga ’Yan Rukunin Band A
- Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar NERC ta yi bayani kan kara kudin wutar lantarki daga N66/KwH zuwa N225/KwH
- An ruwaito cewa karin kudin zai shafi kwastomomin da ke rukunin Band A ne kawai, da ke samun wutar awa 20 a rana
- Hukumar da ke kula da wutar lantarkin ta kuma bayyana cewa za ta rage yawan abokan hulda da ke Band A zuwa Band B
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC) ta amince da karin kudin wutan lantarki ga kwastomomin da ke karkashin rukunin Band A.
A wani taron manema labarai a Abuja ranar Laraba, mataimakin shugaban NERC, Musliu Oseni, ya ce an kara kudin daga N66/KwH zuwa N225/KwH.
Su wa aka kara wa kudin lantarki?
Talabijin na Channels ya rahoto cewa abokan cinikin da ke ƙarƙashin Band A su ne waɗanda ke jin samun wutar lantarki ta sa'o'i 20 a kowace rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oseni ya ce wadannan kwastomomi su na wakiltar kashi 15 ne cikin dari na mutane miliyan 12 da ke amfani da wutar lantarki a kasar.
Ya kara da cewa hukumar ta kuma rage darajar wasu kwastomomi da ke a Band A zuwa Band B saboda gazawar kamfanin rarraba wutar lantarki na basu wutar awa 20 a rana.
Gwamnati za ta kara yawan wutar lantarki
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Oseni yana cewa:
“A halin yanzu mu na da tashoshi 800 na wuta da ke karkashin Band A, amma yanzu za a rage zuwa kasa da 500. Waɗannan tashoshin na ba da wuta ga kaso 15 na masu amfani da wutar lantarki a kasar.
"Hukumar ta ba da umarni na samar da wutar lantarki mai adadin kilowatt 235 a kowace awa ga 'yan Band A daga watan Afrilu."
Ya kara da cewa wannan karin kudin ba zai shafi kwastomomin da ke karkashin sauran rukunan ba.
Majalisa ta hana a janye tallafin lantarki
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa majalisar dattawa ta gargadi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kudirinsa na janye tallafin wutar lantarki.
Sanata Aminu Iya Abbas wanda ya gabatar da kudurin dakatar da Tinubu daga janye tallafin ya kafa hujja da halin matsin rayuwa da ake ciki.
Asali: Legit.ng