Shekara 1 a Mulki: Jerin Ayyukan da Bola Tinubu Zai Kaddamar a Watan Mayu

Shekara 1 a Mulki: Jerin Ayyukan da Bola Tinubu Zai Kaddamar a Watan Mayu

  • Shugaban kasa Bola Tinubu na shirin kaddamar da ayyuka kusan 11 a babban birnin tarayya Abuja domin murnar cika shekara 1 a kan karagar mulki
  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ne ya sanar da hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai, inda ya kara da cewa ayyukan na iya zarce 11
  • An rantsar da Tinubu a ranar 29 ga Mayu, 2023, kuma an nada Wike, jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, ministan Abuja bayan watanni uku

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai kaddamar da wasu ayyuka a watan Mayu a murnar cika shekara guda akan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Abuja: Mummunar gobara ta tashi a gidan shugaban karamar hukuma

Nyesom Wike ya zayyana ayyukan da Tinubu zai kaddamar a watan Mayu
Akalla ayyuka 11 Tinubu zai kaddamar a bikin cikarsa shekara 1 a kan mulki, in ji Wike. Hoto: @officialABAT, @GovWike
Asali: Facebook

Wike, daya daga cikin ‘yan adawa da Tinubu ya nada a matsayin minista, ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a ranar Talata, 2 ga Afrilu.

Ayyuka da Tinubu zai kaddamar

A yayin tattaunawar, tsohon gwamnan na Ribas ya yi magana kan batutuwa da dama da suka hada da siyasar Ribas da kuma dangantakarsa da Gwamna Siminalayi Fubara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Wike, wasu daga cikin ayyukan da Tinubu zai kaddamar sun hada da:

  1. Sakatariyar tarayya (Gini na farko)
  2. Tashar layin dogo ta kwaryar Abuja
  3. Babban titin Kudancin Abuja
  4. Hanyoyin B6 da B12
  5. Gidan mataimakin shugaban kasa
  6. Babbar gadar sama ta Wuye
  7. Hanyar Kudancin Abuja (OSEX)
  8. Babbar hanyar Arewacin Abuja (N20)
  9. Hanyar Guzape 2
  10. Yankin diflomasiyyar Guzape
  11. Hanyoyi biyar masu kai wa zuwa ga tashoshin jirgin kasa na Abuja

Kara karanta wannan

Karfin hali: Uba da dansa sun yi taron dangi, sun yiwa matar makwabcinsu duban mutuwa a Ogun

Yadda dangantakar Wike-Tinubu ta fara

Dangantakar Wike da Tinubu ta fito fili bayan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP gabanin zaben 2023.

Gwamnan jihar Ribas na wancan lokacin ya jagoranci wasu gwamnoni hudu na jam’iyyar da aka fi sani da G5, suka yi adawa da takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.

A ƙasa akwai bidiyon hirar da aka yi da Wike:

"Tinubu nake yi wa aiki ba APC ba" - Wike

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya gargadi masu cewa ya juya wa PDP baya tare da komawa APC ta bayan fage.

Wike ya ce yana nan daram a PDP, kuma shi shugaban kasa Bola Tinubu yake yi wa aiki a ba wai jam'iyyar APC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.