Bola Tinubu Zai Kaddamar da Wasu Manyan Ayyuka a Jihar Ribas

Bola Tinubu Zai Kaddamar da Wasu Manyan Ayyuka a Jihar Ribas

  • Gwaman Wike ya kara dawowa, ya tabbatar da cewa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, zai kai ziyara jihar Ribas
  • Ya ce Tinubu zai kaddamar ga katafariyar gadar sama ta 12 da kuma sabon ginin Kotun Majistire a Patakwal
  • Ana tsammani Tinubu zai kai ziyarar aiki jihar Wike a ranakun 3 da kuma 4 ga watan Mayu, 2023

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya tabbatar da cewa zababben shugaɓan ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai kaddamar da wasu manyan ayyukansa a Patakwal.

Wike ya ce Tinubu ya tsara kawo ziyarar aiki da kuma kaddamar da fitacciyar gadar sama da babu kamarta Rumuola-Rumuokwuta Flyover da sabon ginin Kotun Majirtire a Patakwal ranar 3 da 4 ga watan Mayu.

Wike da Tinubu.
Bola Tinubu Zai Kaddamar da Wasu Manyan Ayyuka a Jihar Ribas Hoto: Nyesom Wike, Bola Tinubu
Asali: Facebook

Gadar Rumuola-Rumuokwuta mai tsawon mita 1007.5, wacce ta haɗa titin Rumuola zuwa titin Ikwerre, ita ce gada ta 12 da gwamnatin Wike ta gina tun daga 2019.

Kara karanta wannan

Somin-tabi: Bidiyon lokacin da Tinubu da Shettima ke kaura zuwa gidan gwamnati

The Nation ta rahoto cewa gwamna Wike ya faɗi haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kelvin Ebiri, ya fitar ranar Laraba, 26 ga watan Afrilu, 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya sanar da cewa shugaban ƙasa mai jiran gado zai kawo ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Patakwal, babban birnin jihar Ribas domin buɗe ayyukan.

Vanguard ta ce Wike ya tabbatar da ziyarar da Tinubu zai je Ribas yayin da yaje duba aikin gadar Rumuola-Rumuokwuta da kuma ginin Kotun Majistire a Patakwal ranar Laraba.

Wike ya ce:

"Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, muna tsammanin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa zai zo ranar 3 da 4 ga wata mai kamawa domin ya kaddamar da gada ta 12 da kuma ginin Kotun majistire."
"Kun ga yadda ginin Kotun ya kasance da kuma yadda ya zama abin sha'awa. Mun yaba wa ɗan kwangilan wanda ga sauke nauyin da aka ɗora masa kuma a kan lokaci."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Fitaccen Attajirin Da Ya Fi Kowa Kuɗi a Afirka Ya Kaiwa Tinubu Ziyara, Hotuna Sun Bayyana

Aliko Dangote, Ya Ziyarci Bola Tinubu a Abuja

A wani labarin kuma Hamshaƙin Attajirin Dan Kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, Ya Ziyarci Zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu a Abuja

Futaccen Attajirin ɗan kasuwa nan ɗan asalin Kano, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ziyarci shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu, yayin da ake tunkarar ranar rantsarwa.

Tinubu ya karbi bakuncin Ɗangote tare da wasu manyan jiga-jigan APC ciki har da kakakin majalisar wakilan tarayya da gwamna mai ci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel