Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Ciyo Bashin Makudan Kudi? Gwamna Ahmed Ya Fayyace Gaskiya

Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Ciyo Bashin Makudan Kudi? Gwamna Ahmed Ya Fayyace Gaskiya

  • Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya fito ya yi martani kan rahotannin da ke cewa gwamnatinsa ta ciyo bashin maƙudan kuɗade
  • Mai girma Gwamnan ya bayyana cewa tun lokacin da ya hau kan karagar mulki, jihar ba ta ciyo bashin ko sisin kwabo ba
  • Ya yi nuni da cewa dukkanin ayyukan da ya gudanar a jihar, an yi su ne da kuɗaɗen da ake samu daga asusun tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, ya musanta karɓar bashi daga ƙasashen waje domin gudanar da ayyukan raya ƙasa a jihar.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga wani rahoto da aka fitar, inda aka sanya jihar Sokoto cikin jerin jihohin Arewacin Najeriya da suka ciyo bashi domin gudanar da ayyukan raya ƙasa.

Kara karanta wannan

Daga karshe Wike ya bayyana inda aka kwana kan rikicinsa da Gwamna Fubara

Gwamnan Sokoto ya musanta ciyo bashi
Gwamna Ahmed Aliyu ya ce gwamnatinsa ba ta ciyo bashi ba Hoto: @Ahmedaliyuskt
Asali: Twitter

Gwamnan, wanda ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda jihar Sokoto ta shiga cikin jerin, ya ce gwamnatinsa ba ta taɓa karbar wani bashi daga ciki ko wajen ƙasar nan ba, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bashin nawa gwamnatin Sokoto ta ciyo?

A kalamansa:

"Bari in bayyana ƙarara cewa ban taɓa ƙarbar bashi a wurin kowa ba tun da muka hau kan mulki.
"Na yi mamaki da na ji an saka jihata a cikin jihohin Arewacin Najeriya da suka karɓi bashin ƙasashen waje domin bunƙasa jihohinsu.
"Hakika rahoton na yaudara ne, kuma ina sa ran za su tabbatar da bayanan da suka ce sun samu daga hukumar kula da basussuka kafin su fitar da rahoton.

A ina gwamnatin ke samun kuɗi?

Gwamnan ya ci gaba da cewa dukkan ayyukan da ya gudanar a faɗin jihar, an biya su ne ta hanyar amfani kuɗin da jihar take samu na wata-wata daga asusun tarayya ko kuɗin shiga da jihar samu, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi abin da zai hana Tinubu yin shekara 8 kan karagar mulki

A cewarsa:

"A yanzu, ba ma buƙatar wani lamuni kafin mu aiwatar da ayyuka saboda muna amfani da kuɗin jihar yadda ya dace."

Gwamna Ahmed ya faranta ran ma'aikata

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya amince da biyan rabin albashi ga ma'aikatan jihar da 'yan fansho.

Gwamnan ya amince da biyan albashin ne kyauta ga dukkan ma'aikata tun daga malaman makarantun firamare da ma'aikatan kananan hukumomi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng